Saturday, April 29, 2023
ARZIKI RIGAR ƘAYA (1)
Tuesday, October 18, 2022
Karen Bana...
Friday, May 19, 2017
NAZARI KAN ASALIN HAUSA
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
08060869978
Kashi na uku
Farfesa Umar El zakzaky Al Bahaushe yace" kwayoyin halittar Fir'auna Seti, wannan daya yayyanka yahudawan zamaninsa, da kuma na magajinsa Fira'una Remesis II, wanda yayi zamani da Annabi Musa A.S sunyi kamanceceniya da kwayoyin halittar mutanen kano na yau, musamman ma nacikin kwaryar badala."
Sai dai Farfesa Muzzah Jibrin, Farfesa Abdullahi Elkanawy da wasu masana da dama sunyi watsi da wannan bincike. Ga abinda ya fito daga makalar masanan kamar yadda suka gabatar a wani taro daya gudana a Arewa House dake kaduna:
Kuskure ne a hada asalin wancan Fir'aunan da kano tunda Gawar Mornoptah, dan Fir'auna Remeses II, fir'aunan da aka halakar a ambaliyar ruwa yayin da yake bin sawun Annabi Musa A.S don ya halaka shi, wadda Masani Loret ya gano a shekarar 1898 a tsohon birnin Thebes ta nuna cewar kwayoyin halittar ta sunfi kamanceceniya dana mutanen egypt ne ba mutanen kano ba".
A wani kaulin kuma, masanan sunyi hasashen cewa kwayoyin halittar mutanen zariya dana kabilar Gwari da Igala suma sunyi kamanceceniya da juna, wanda hakan na nuni da cewar kodai kabilun asalinsu a zariya suke da zama, ko kuma al'ummar kabilun ne suka kafa garin na zaria lokaci mai tsawo daya shige, don haka yanuwan juna ne kenan. Muna kuma iya cewa daga jikin mutum guda kabilun suka fita.
Amma maganar su da sukace sun auna wasu ɓuraguzai na kasusuwan mutanen dake kwance a wasu makabartu a kano, har kuma sun gano cewar mafi yawan kwayoyin halittar mutanen kano yafi nuni dana Sharifai, kamar akwai siyasa a ciki.
Tabbas, tarihi ya nuna cewar a wajajen karni na goma sha uku, wangarawa karkashin Sheik Abdurrahman Zaiti tare da wasu malamai kimanin arbain irinsu Modibbo sheshe, Mandawari, Limamin Madatai, Limamin Jujin 'yan labo sunzo kano har ma suka kawo musulunci garin. Lokacin Sarkin Kano Yaji dan Tsamiya ke bisa gadon sarauta.
Sai kuma a karni na goma sha biyar zamanin Sarkin Kano Rumfa Akace wani balarabe masani mai suna Imam Maghili ya ziyarci kano shima da wasu jama'a tasa. Daga baya ma ance yabar wasu daga zuriyarsa anan kano, wadanda su ake kira Sharifai zuwa yanzu.
Marubuci, marigayi Maje Ahmad Gwangwazo ya kawo wata muhimmiyar gaba a shafi na 22 na littafinsa mai suna Wangarawa Sun iso Kano, inda yake cewa "Sheik Abdullahi Ilorin ya nuna cewar tun a karni na goma sha ɗaya wangarawa suka fara bazuwa suna yaɗa musulumci a afirka ta yamma. Yace su wangarawa kasarsu ta farko misira(Egypt). Yace asalin mazaunan kabilar Sundiata da asalin kabilar Kakan Mansa Musa da asalin kabilar Songhai irinsu Askiya Muhammad kenam, tarihi ya nuna duk a misira suke kafin su iso Mali, inda mafi yawan masu tarihi ke cewa daga Mali wangarawa sukazo, amma Mali din
ma zuwa sukayi".
Sai dai, koda auratayya ta wanzu tsakanin wangarawa da larabawan da suka sauka a kano da kanawa bakaken fata na lokacin, da wuya ace an samu kwayoyin halitta sunyi irin wannan mamakon rinjayar. Domin kuwa kano tun asali garin bakaken fata ne ba farare ba, ba kuma a taɓa samun cewar an maye mutanen kano da wasu mutanen ba, don haka faɗin cewar kwayoyin halittar kanawa ya nuna su sharifai ne ba lalle ya zamo ya inganta ba.
Amma tana iya yiwuwa, anyi rashin sa'a, ɓuraguzan da aka samu a makabartun waɗanda akayi wannan gwajin dasu (sample) na Wangarawa da larabawan ne dana zuriyarsu wadanda watakila sun cakuɗu da bakaken fata, don haka binciken bai iya bada labarin ɗaukacin mutanen kano ba, tunda dokar irin wannan binciken ta nuna cewa wajibi ne abubuwan da za'ayi bincike akansa su zamo suna wakiltar ɗaukacin abinda ake magana akansa.
Wani abin lura ma anan shine shigar siyasar addini acikin dukkan binciken.
Munji bincike na farko ya nuna cewar Fir'aunan daya kashe jarirai ɗan kano ne, don haka wasu ke ganin hakan kamar kaskanci ne ga kanawa, shiyasa sukuma suka wanke kanawa da cewar asalinsu sharifai (jikokin fiyayyen halitta) ne..
A hakika dai, bamu da karan nunawa ga waɗancan Malumma masu girma, amma wajibin mune mu karɓi gaskiya komai ɗacinta dangane da asalin mu. Maganar addini ba zata sa mu ɓoye asalin muba, tunda da ayyukan mu akace za'ay mana hisabi bada asalin muba. Rashin ingancin binciken na farko shine kurum hujjar da zatasa muki aminta dashi amma ba laifiɓ da firaunan ya aikata ba.
Akwai binciken masana dake cewa Kwayoyin halittun Firauna Remesis II yafi kamanceceniya da kwayoyin halittun mutanen Afirka ta tsakiya a ma'auni na farko, daga nan sai mutanen kasar south Africa a ma'auni na biyu, sannan mutanen Afirka ta yamma inda hausawa suke a ma'auni na uku. Wanda hakan ke nuna alakar hausawa da wancan firauna tayi tazara da shekaru masu nisan gaske... (Watakila sai kowacce kabila daga cikin biyun ta tike da Annabi Nuhu ko Annabi Adamu za'a ɗiga aya)
Sai dai kuma, akwai tsohon zance dake nuna kwararowar misirawa izuwa yankin afirka ta yamma a tsahon zamani daya shuɗe. Watakila tun zamanin Annabi Musa A.S hakan ta faru, ko kuma wani lokaci kafin haka, domin kuwa labarin baka yana nuna cewar garin Auyo dake jihar jigawa ya kafu tun kafin Haihuwar Annabi Musa A.S, sai dai kuma karancin tarihin da muke dashi akan kabilar Auyokawa da akace sune suka kafa garin ke hanamu gane alaka ta jini ko ta sadarwa da wayewa a tsakanin mutan garin da kuma misira tun a wancan tsohon zamani.
Da alama dai, Magana mafi inganci bisa kwayoyin halittar hausawa shine wanda wasu gungun masana suka gudanar akan hausawa mazauna sudan.
Da fari, Binciken ya nuna cewar kashi arbain na kwayoyin halittun hausawa dake zaune a sudan sunyi dai-dai dana kabilun sudan ɗin. (Hassan et al 2008)
Akwai kuma makamancin binciken daya nuna cewa kwayoyin halittar Hausawa ya nuna cewa su 'yanuwan juna ne da wasu kabilu masu amfani da yaren Nilu mazauna Nigeria, Cameroon, Central Chad da kuma kudancin Sudan. (Toshkoff et al 2009).
Binciken ya nuna cewar asalin yaren hausa, da yarukan waɗancan kabilu guda ɗaya ne saboda alakar yarukan da aka gani suna dashi da juna.
Bakaken fatar chadi dana kamaru duk ana tsammanin sun gangara yankin ne shekaru da dama da suka gabata daga daular sudan. Sukuwa mazauna sudan, duk da gaurayuwar kwayoyin halittun larabawa dana sauran kabilu a tattare dasu, an gamsu da cewa su jikokin tsoffin bakaken fata ne na tsohuwar daular nan ta 'Meroa' data shahara a duniya wadda ta wanzu a sudan ɗin.
Ta haka, sai ake hasashen cewa kakannin hausawa da kakannin sudawa da kakannin wadancan kabilu mazauna cameroon da chadi sun fito ne daga tsatson Uba daya, amma hijirar data rinka aukuwa tsakankanin mutanen_da shine sanadiyar rarrabuwarsu ta yadda yanzu kowa yayi nesa da kowa. Hasashen kuma na nuna cewar wannan rarrabuwa ta auku akalla da shekaru dubu biyu baya zuwa sama, tayadda a iya wancan lokacin ne kowacce kabila tayi chakuduwa da sauran kabilu har kashi sittin na kwayoyin halittar su ya sauya, kashi arbain ne kadai zuwa yanzu bai jirwaya ba. Babbar hujjar hakan itace samuwar wasu kabilun daga jikin waɗancan na ainihi, tayadda ansan ana ɗaukar tsawon lokaci kafin faruwar hakan. Sai kuma tsawon zamanin da daular bakaken fatar tayi a raye har kuma ta rushe. Kamar abinda Marubuci Morton H. Fried ya faɗa a littafinsa mai suna 'The Notion of the Tribe' cewar akwai kabilu na ainihi (primary tribe), akwai kuma kabilu samammu daga na ainihi (secondary tribe).
Don haka idan har kabilun yahudawa guda goma sha biyu sun fita daga jikin Annabi Yakuba A.s (Israel), to muna iya cewa kabilar Annabi yakuba da yarensa shine kabila ta ainihi, samammun kabilun kuwa sune waɗanda 'ya'yansa sha biyu da jikikinsa suka ɗauka bayan rarrabuwarsu ga wajen zama
Kuma ana iya samun kabilu sama da ɗaya mai amfani da yare ɗaya, amma dai anfi samun kowacce ɗlkabila da irin nata yaren gami da ɗabi'a wanda take samarwa kanta-da-kanta gwargwadon wurin zamanta da aɓin bukatarta da kuma abubuwa makusanta da take dasu.
Sannan tana iya yiwuwa ma, kafin Hausa ta zama hausa, sai da wasu kabilu suka firfita daga asalin kabilar ta ainihi. Tunda dai zamu gamsu cewa hausa daga wata kabilar ta cire kanta.
Kowa dai ya rike cewar Maguzawa sune asalin hausawa, har ana kallon kalmar hausa a matsayin bakuwa. Don haka yadda akayi hasashen alaka ta jini tsakanin kabilun maguzawa, Gwandara, Ngizzim da kuma Bole shima abin nazari ne wajen gane asalin uban jinsi wanda hausawa suka fito daga gareshi, tunda masana sun nuna cewar kwayoyin halittu gami da yaruka duk sunyi kaman-ce-ceniya da juna.
A Littafin tarihin Gwandara da Dr. Silvestri O. Ayihai ya wallafa mai suna 'The History of Gwandara towns and villages' ya nuna cewar sai da kabilar Gwandara ta jima tana zagaye-zagaye daga nan zuwa can, suna Farauta karkashin jagorancin shugabansu mai suna Dan Baba sannan suka riski wani waje mai suna Kupai sannan suka fara zama. Daga nan ne sannu a hankali suka samar da masarautar su gagaruma.
Mu kuwa anan kasar hausa, an samu labarin baka cewar asalin Gwandara hausawa ne da suke zaune a kano, wai lokacin da Musulunci yazo sukace sam Gwanda (suyi) rawa da (suyi) Sallah, don haka suka bar kano zuwa wani wajen da zama.
To idan ma wannan labarin na Gwanda-rawa-da sallah bai inganta ba, wancan binciken na kwayoyin halitta ya isa ya nuna mana cewar zamani mai tsawo daya gabata kabilun biyu sun zauna da juna a matsayin yanuwan juna.
Kabilar Ngezim kuwa ance sune asalin wadanda suka soma zama a tsohon birnin Ngazargamu na daular Kanem. Suma dai ance sun warwatsu a wannan yanki da hausawa suka mamaye ayau, amma dai yankunan Yobe, Borno da Jigawa nan ne tsohon wurin zamansu.
Haka ma kabilar Bole, wadda akace suma mafarauta ne waɗanda suka mamaye yankunan Bauchi, Gombe, Yobe da kuma Jos. Zuwa yanzu ana ganin kamar sun saki al'adunsu da yarensu sun ɗauki na hausawa.
Su kuwa maguzawa ance manoma ne, amma tana iya yiwuwa sun jarraba noma ne sukaga yagi farauta riba don haka suka yadda sana'ar kakannin nasu.
To ai waɗanda suka fara zama a dutsen dala na garin kano ma ance mafarauta ne.. Wai har taron shiga farauta ma akeyi a bakin dutsen lokaci zuwa lokaci, inda manyan mafarauta ke zuwa daga sassa mabanbanta.. Kenan farauta sana'ar kakannin waɗannan alummomin ne baki ɗaya, don haka suka kasa sakinta, tayadda koda sun zauna a wani wuri na wani lokaci sun jarraba wani abin, da zarar sun tashi daga wurin kanta suke sake komawa..
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
Thursday, May 18, 2017
NAZARI KAN ASALIN HAUSA
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
08060869978
Kashi na biyu.
ASALIN JINSIN HAUSAWA
Tana iya yiwuwa, littattafan mu na addini sune suka fara kawo mana tarihin asalin jinsi da rarrabuwarsa. Saboda wannan wani tarihi ne daya faru wanda indai ba baiwa mutum iliminsa akayi ba, zaiyi wuya ya iya wassafa yadda tarihin ya faru.
Ance Annabi Adamu da Matarsa Hauwa'u sune mutane na farko a duniya. Sune suka rinka haihuwar 'ya'yaye biyu-biyu daki-daki, tare da haɗa aure tsakanin mace ɗaya da namiji ɗaya daga tagwaye mabanbanta, watakila wannan haihuwar tasu itace asalin kabilu, gamin gambizar kuwa shine asalin dangantakar jinsi da kuma rarrabuwar sa.
Idan ma ba haka ba, ko labarin Annabi Nuhu A.S ya nuna cewar ya haifi 'ya'yaye uku ne. ƊAkace Hamu shine ya haifi bakin mutum na farko a duniya, daga jikinsa kuma zuriyar hindu ta fito. Samu shine na biyu wanda akace daga jikinsa turawa suka fito, sai kuma Yafisu wanda akace daga tsatson sa kabilun birnin Sin suka ɓulɓulo. Don haka, tanan kaɗai muna iya hasashen cewa cakuɗuwa ta silar auratayya da sauran kabilu ne silar haifar da wasu sabbin kabilun.
Babban labarin dai shine, akwai ilimi na zamani dake bada damar fahimtar kwayoyin halitta tayadda har ake gane wane nada alaka ta jini da wane, da haka kuma muke son fahimtar hausawa da asalin waɗanda suke da alaka dasu, in yaso daga bisani sai mu kwatanta kokarin bin diddigin shekarun da rarrabuwa ta auku a tsakanin su.
A bisa wancan ilimi na kwayoyin halittu (Genetic), dukkan wani ɗan adam dake doron kasa nada kwayoyin halitta waɗanda ana iya cewa kashi 99.5 na zubin kamanceceniyarsu ɗaya yake da juna. Wannan ke tabbatar mana da wancan ilimin da aka saukar mana cewa mutum ɗaya ne asalin ɗaukacin mutanen duniya, daga gareshi dukkansu duka fito.
Abu na gaba shine, kusan muna iya cewa a yanzu babu wata kabila da zaka samu 'yan cikinta da kwayoyin halitta zubi ɗaya tsura, sai dai zaka samu kaso sama da hamsin iri kaza ne, sannan da wasu kashe-kashen na sauran kabilu kaɗan-kaɗan aciki.
Wani masani Ronald Fisher yayi bayani gwargwadon yadda zamu gane bisa tafarkin masanin ilimin kwayoyin halitta Gregor Mendel a littafinsa mai suna 'The Genetical theory of Natural Selection' inda yake cewa dalilai biyu ne kesa wannan cuɗanyar tsakanin kwayoyin halittu. Dalili na farko shine, yanayin yadda ake gadon su kansu kwayoyin halitta na sanyawa na wancan yasha banban dana wancan koda kuwa uwa ɗaya uba ɗaya suke, domin ko a siffance, akan iya ganin uba da 'yayansa uku, yaro na farko yayi kama da mahaifiyarsa, na biyu yayi kama da ubansa, yayinda na uku ya ɗauko kamannin kakansa.
Dalili na biyu kuwa shine cuɗanyuwar kwayoyin haluttun ta hanyar auratayya. Watau, ɗan wannan kabila ya auri yar waccan kabila. Sai kaga kwayoyin halittar waccan kabila dana wancan sun haɗu a kabila ɗaya, amma sai akalli inda sukafi rinjaya ayi hukunci dashi.
ASALIN JINSIN LARABAWA DA YARABAWA
Yana da kyau, kafin mu fahimci asalin jinsun mu mufara fahimtar ilimin dake cikin asalin kabilu makusantan mu.
Su dai larabawa, wani bincike mai taken 'National Geographic's Genographic' da aka gudanar a shekarar 2005 ya bayya cewa akalla duk wata kabila balarabiya ta fito daga cikin yankuna huɗu ne.
Yanki na farko shine Arabia.
Yanki na biyu shine Arewacin Afirka.
Yanki na uku shine gabashin Afirka.
Sai yanki na huɗu watau Asia.
Sai wannan binciken ya ɗauki wasu kasashen larabawa tare da bayyana yadda asalin su ya kasance.
Misali, Daga ciki an ɗauki kasar Tunisia, wadda akace kaso 88 na kwayoyin halittar mazauna kasar ya nuna cewar suna da alaka ta jini da sauran larabawan Arewacin Afirka. Amma akwai sirki na larabawan Arabia da kaso 5, da sirki na turawa da kaso 4, da kuma sirkin bakaken fata mazauna afirka ta yamma da kaso 3. Wannan sirkin nuna cewar an samu auratayya da gamin gambizar kwayoyin halittu shekaru da dama da suka wuce a tsakanin jinsosin da aka zayyana a sama.
Labarin kusan haka yake ga Yarabawa domin kuwa wani bincike da wasu masana Adebuwale Adeyemo na jamiar Ibadan, Chenchen Yianxiu na Cibiyar bincike ta 'National Human Genome' da kuma Charles Rotimi na jamiar Horward suka gudanar, sun samu cewar kwayoyin halittun Yarabawa, ɗaya ne dana kabilun Igbo, Akan, da Gaa-Adangbe.
Hakan na iya nufin cewar Asalin kabilun mutum ɗaya ne, daga 'ya'yansa ko jikokinsa aka samu rarrabuwar waɗannan kabilu har ma dana yare, tunda binciken yayi hasashen cewa duk yarukan kabilun suna da alaka da juna, asalinsu guda ne, daga bisani suka rarrabu, duk da dai binciken bai nuna sauran kabilun da suka shigar da kwayoyin haluttun su cikin na waɗannan ɗinba.
JINSIN HAUSAWA
Abinda wani bincike dangane da bakaken fata yayi hasahe shine shekaru masu yawa da suka gabata, mafi yawan bakaken fata suna wuri ɗaya ne a zaune, kuma tana iya gaskatuwa Cewa mutum ɗaya ne uba wanda daga jikinsa duk kabilun bakaken fata suka fito. Amma dai, anyi hasashen cewa tun shekaru dubu sittin zuwa dubu tamanin baya bakaken fata suka soma baro wancan mazaunin nasu na asali tare da fantsamuwa a sassan duniya musamman afirka ta yamma. Daga waɗannan zuriyar ne kuma akafi kyautata zaton bakaken fata Hausawa sun fito.
Babu jimawa, farfesa Umar Elzakzaky Al-Bahaushe yayi hasashen cewa kwayoyin halittun hausawa dana tsoffin misirawa sunyi kamanceceniya, har ma yace yana kallon kamar firaunan dayayi zamani da Annabi Musa A.S bahaushe ne.
Inaga zamu karu da ilimi idan muka kalli zancen nasa da kuma martanin hujjoji da masana suka bashi dangane da musanta wannan magana tashi...
Za mu ci gaba.
Sunday, May 14, 2017
NAZARI KAN ASALIN HAUSA
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
08060869978
Kashi na ɗaya
Gabatarwa
Da Sunan Allah mai Rahama mai jinkai.
A ɗaukacin tsoffin biranen kasar hausa, kukoki nanan burjuk a inda akasari ya zamo gonaki a yanzu. A wasu tsoffin biranen duniya, tsoffin gine-gine da tsoffin masana'antu, ko kaburbura ke nuna rayuwa ta wanzu a waɗannan wuraren.
Idan har Kukoki ne kaɗai babbar shaidar da zamu iya gane cewa rayuwar hausawa ta taɓa wanzuwa shekaru da dama da suka gabata a wani wuri saboda kila tun asali hausawa basa manyan gidaje da kere-kere waɗanda buraguzansu zasu samu tsira har zuwa yanzu, to ya kamata muyi nazarin labarun da waɗannan kokuki tsofaffi suke bayyanawa a garemu.
A kabilar Nkwici ta Kasar Malawi, ana kiran bishiyar Kuka da sunan 'Bishiyar Rayuwa'. Saboda a cewar su, bishiyar na baiwa mazauna kauyuka mafaka a zamanin yaki yayin da mahara suka nufosu. Sannan ana amfani da ganyenta da kuma 'ya'yanta don abinci gami da magani. Har ila yau, akwai canfe-canfe da dama a tattare da ita.
A kasar Madagaskar kuwa, an samu wata gagarumar Bishiyar kuka mai kimanin shekaru dubu uku, tsayinta zai tasamma kafa ɗari, faɗin ta kuwa an kiyasta sai mutane akalla goma sun kama hannuwan juna zasu iya rutsata. Mutanen yankin suna matukar girmama wannan kukar, har suna kiranta da 'Bishiyar Mutuwa', domin anasu fahimtar, duk wanda ya mutu a yankin, nan ruhinsa ke zuwa ya zauna.
A gundumar Linpopo dake South Africa, an samu wata gagarumar Bishiyar kuka. Tsayinta da faɗinta duk sun haura kafa talatin da biyar kowanne. Tana da kogo, wanda aka ayyana cewar mutane acan baya sun maida kogon wajen fira ko wajen fakewa, domin an samu wasu abubuwa irin na sojin-da da kuma na mu'amala aciki, binciken 'carbon dating' na masana kimiyyar zamani ya kiyasta cewar bishiyar takai kusan kimanin shekaru dubu shida a raye.
Akwai kuma sirrin kuka da Marubuci ɗan kasar faransa Richard Mabey ya ruwaito a littafinsa mai suna 'The Caberat of Plant' cewar Giwaye da manyan namun daji suna zuwa jikin kuka susha ruwa. Wai da zarar sun hangota alhali suna cikin ɗimuwar kishi, sai aga sun nufeta da gaggawa, sannan su yage bayanta su soma lasa. ƊDaga bisani bincike ya nuna cewa bishiyar na iya tanajin ruwa sama da lita dubu ɗari gwargwadon girmanta da adadin shekarunta.
Idan waɗannan abubuwan da mukaji daga Sassan duniya gaskiya ne, shin me muka samu game da kuka a kasar hausa? Kpɓkuma wane labari kokokin kasar hausa suke bamu?
Irin waɗancan manyan kukoki nanan barbaje a kasar hausa. Wasu ma an lakaba musu sunaye mabanbanta, watakila na mutanen da sukafi zama a karkashin kukokin ne. Misali, akwai Kukar Boka, Kukar Gajere, Kukar kwanɗi.. Da sauransu.
A bisa tsoffin hausawa da fulani da muka tambaya, kusan ɗaukacin su sun tafi akan cewa duk kukar daka gani da kanta ta fito ba shukata akayi ba. Wannan fa ana magana ne akan matasan kukoki waɗanda muke ganin basu tara shekaru da dama ba, amma game da manyan kukoki masu alamar shekaru, Tsoffin sun tabbatar mana da cewa tasowa sukayi suka gansu.
Haka nan, ana iya lura cewar a gonaki da dazuzzuka inda babu mutane dake rayuwa a wurin, ba kasafai bishiyar kuka ke fitowa ba. Amma kuma mafi yawan unguwannin hausa na tsofgin garuruwa na ɗauke da bishiyar kokoki. A wani sa'in ma, akan samu bishiyar kuka a kowanne gida, ko kuma a bayan gidan.
Watakila, hakan na nuna cewar sai da mutane suka fara zama a wannan wuri sannan kukokin suka fito. Idan kuwa hakan ta tabbata, to zamu iya sanin shekarun kukoki a kasar hausa ta hanyar binciken zamani, sannan da watakila zamu iya sanin jimawar lokacin da hausawa suka fara zama a wannan wuri, tayadda daga bisani zamu gane gari mafi tsufa a kasar hausa.
Idan kuma ta tabbata cewar yawan bishiyoyin kuka ke nuni da yawan mutanen da suka rayu a gari, da shima zai zamo mana ma'auni mafi sauki don gane tsoffin garuruwan da sukafi tumbatsa da mutane shekaru aru-aru da suka wuce..
Za mu ci gaba...
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
TARIHIN GOBIR: DA YADDA GOBIRAWA SUKA RISKI KASAR HAUSA
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Kasar gobir na ɗaya daga cikin kasashen hausa na ainihi, ance ita ɗin tsohuwar daula ce kuma wata babbar kasa ce da tayi iyaka da Agades daga arewa, tayi iyaka da Zamfara daga Kudu, tayi iyaka da Mayali daga Gabas, sannan kuma daga yamma tayi iyaka da Konni.
Amma magana anan itace, asalinsu ba hausawa bane tunda wasu nacewa asali waiƴ daga gabas ta tsakiya suka fito musamman ma Misira, inda ake da yakinin cewa Sarakuna ukku daga cikin sarakunan Misira gobirawa ne.
Sarkin Gobir Mai daraja Alhaji Abdulhamid Balarabe Salihu ya taɓa faɗar asalinsu a wata fira da jaridar 'Daily Trust' tayi dashi, shine yake cewa:
Gobirawa sun zone daga misira (egypt). Har Yace su jikokin Annabi Nuhu A.S ne kuma sun bar misira saboda wahalar mulki na sarakunan lokacin. Shine suka sauka a wani wuri mai suna Gubur. Daga nan ne suka samo sunan Gobir.
Yaci gaba da cewa daga baya sun isa Yemen, sunyi yaki sosai a kasar saboda su suna da jinin yaki da jarumta. Daga nan kuma sai suka isa libya, a haka suna matsawa har suka zo wani gari mai suna Azbin inda yanzu mutanen Taureg suka mamaye.
Da suka bar Azbin sai suka shiga sahara, har suka kafa wani gari mai suna Magali, daga baya sai suka bar garin izuwa wani mai suna Surukul (dukkansu yanzubsuna jamhuriyar Niger ne). A hankali suka riski birnin lalle da gwararramu a karni na 15 zuwa na 16. A lokacin kuwa, Sarkin zamfara Abarshi ke mulki wanda yake da zama a Katanga, kuma an samu har ya auri ɗiyar sarkin Gobir mai suna Fara, wadda ta haifi Sarkin gobir Ibrahim Babari.
Kafin Babari ya zamo sarki, ai sai dayayi faɗa da Sarkin Zamfara na lokacin kuma yaci karfinsa. Akan haka sarkin Zamfara ya kuduri niyyar halakashi, amma sai yayarsa ta maido dashi kasar mahaifiyarsu watau Gobir, a haka kuma har ya zama sarki (Watau yayi gado ta wajen Uwa).
Babari ya roki Sarkin gobir ya bashi wuri a yankin Zamfara inda zai zauna, amma sai aka gargaɗi sarkin Zamfara da cewa kul ya baiwa Babari gurin zama domin nan gaba zai iya mamaye zamfara dukkan ta, ai kuwa daga bisani hakan ne ya faru, da yaki ya ɓarke a wajajen karni na 16 zuwa na 17, sai da Goburawa suka cinye har Alkalawa da yaki. (abinda ke nufin inda suke zaune ayau asali kasar zamfara ce)
Sarkin Gobir Abdulhamid ya kara da cewa " A lokacin Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo (Karni na 17), ance an ruwaito cewa Ko zakaru basa cara sabida jarfin tsafinsa, kuma aduk yake-yaken da sukeyi, gobirawa basu taɓa mika wuya ba. Ance sunfi gwammacewa a kashe su akan su mika wuya, shiyasa ake musu kirari da 'Gobir gidan faɗa'.
Sarkin yace " Bawa jan Gwarzo bai taɓa yaki da Shehu Usmanu ba A zamanin jihadi, maganar gaskiya ma itace shehu ya koyar da 'ya'yan Bawa, ciki harda Yunfa, Atiku, Bello da Mayaki. Ance ma saida shehu yayi musu nasiha da kada su bari a samu rarrabuwar kawuna a tsakanin su.
Sarkin yace " Mutanen dake kusa da Bawa sune suka haɗa kiyayya a tsakanin su, wanda yayi silar shehu yabar Alkalawa, daga baya kuma yaci gaba da jihadi a sassan sokoto.
Dan gane da tsagun gobirawa, Sarkin yace asali basu da tsagu a fuska, amma sabili da yake-yake ne yasa suka rinka tashi daga nan zuwa can, don haka suka ɓullo da tsagu domin su rinka shaida junansu.
Thursday, May 11, 2017
TARIHIN FULANI: Nasabar Toronkawa.
Suka yi yawa kwarrai, har lokacin da aka aiki ukubatu yaki Afirka, ya sadu dasu. Sai suka shiga addinin islama ba tare da anyi faɗa ba. Ukubatu ya auri ɗiyar Sarkinsu, sunanta Bajju Mangu. To su Toronkawa jinsi ne da suka fito daga zuriyar Ramo, ɗan Isa, ɗan Ishaku, ɗan Annabi Ibrahim (AS).
Daga baya zuriyar Ukbatu ta yawaita.
- Kashi na biyu suka koma Falgu inda suka soma zama da fari
- kashi na uku suka yo gabas suka tsammaci zasu riski 'yanuwansu Larabawa saboda Ubansu balarabe ne. Wasu cikinsu sun iya komawa kasar larabawa, wasunsu kuma sun kasa basu karasa ba. Sunan babban su Dunurundi.
Wednesday, November 30, 2016
LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Littafi ne da ya kunshi sabuwar fassarar dadadden littafin Larabawan nan mai suna ALFULAYLAH WA LAYLAH. An inganta fassararsa da daidaitacciyar Hausa, da kowane Bahaushe zai iya karantawa kuma ya fahimta.
Littafi ne da ya kunshi hikayoyi masu ratsa zukata, wadanda suka kunshi, tsantsar soyayya, jaruntaka da yaki, tsafe-tsafen mutanen dauri, duniyar aljanu da maridai, tatsuniyoyi, wa'azi da nasihohi, makirce-makircen maza da mata. Littafin ALFULAYLAH tumbin giwa ne, wanda babu irin labarun da babu a ciki.
Tuni mujalladi na farko ya shiga kasuwa. Maza hanzarta domin ku mallaki naku. Za a same shi a manya da kananan kantunan sayar da littattafai.
Haka kuma ga masu son karanta littafin dukkansa a Facebook (tun daga dare na 1 har zuwa dare na 1001), mun zube shi a cikin zauruka (groups) goma sha bakwai a Facebook, wanda za a iya biyan Naira dari biyu kacal (N200) domin shiga kowane zaure. Kada ku bari wannan dama ta wuce ku.
A tuntubi daya daga cikin masu fassarar, domin karin bayani game da yadda za a samu littafin, ko yadda za a biya kudin rijista:
Farfesa Malumfashi:
08035924022
Danladi Z. Haruna:
08030764060
Bukar Mada:
08021218337
Monday, July 7, 2014
DARE DUBU DA DAYA
Amincin Allah ya tabbata a gare ku.
Ganin yadda jama'a suke ta nuna sha'awarsu game da hikayoyin wannan littafi na Alfu Laila wa Lailatun ko kuma DARE DUBU DA DAYA, shi ya sa ni (Bukar Mada), da Professor Ibrahim Malumfashi, da wani marubuci mai suna Danladi Haruna, muka yanke shawarar samar da cikakken wannan littafi (tun daga dare na 1 har zuwa Dare na 1001) da Hausa domin al'ummar Hausawa su sami abin karantawa.
Littafin DARE DUBU DA DAYA shahararen littafi ne na Larabawa da ya yi fice a fadin duniya gaba daya. An fassara shi cikin harsunan duniya da yawa, ciki har da Hausa. Na hausar an fassara shi fiye da shekara dari (100) da suka wuce, lokacin babu Typewriter ko computer a kasar Hausa, wani bature ne mai suna Frank Edgar ya rubuta tare da taimakon wasu Malamai na kasar Sokoto, don haka da hannu aka yi rubutun (kamar yadda kuka ga samfur din rubutun a cikin wannan hoto).
Rubutun na nan a cikin taskar ajiyar tsofaffin bayanai na Kaduna, fayil goma sha hudu (14). Kowane fayil akwai takarda 700 zuwa 800 ciki. Shi ne Kamfanin NNPC suka buga littafi biyar daga fayil na farko (duk littafi daya na NNPC ana sayar da shi N500 ne a kasuwa, idan kuka hada littafi biyar, watau fayil guda kenan, kudinsu ya kama N2,500). Sauran fayilolin ba a kuma kula su ba, balle a buga su, su zama littattafai.
Ganinirin muhimmancin aikin a Adabin duniya shi ne muke wannan yunkurin yanzu na ganin mun juya wannan rubutun hannu, na dukkan fayilolin 14, zuwa rubutun computer, sannan mu buga littattafan don sayarwa ga al'umma. Hoto (photocoy) kawai na takardun da muka yi, sun lashe kudi sama da dubu saba'in(N70,000). Kenan wannan ba karamin aiki ba ne, sai an nemi gudummawa ga jama'a.
Daga nan sai muka yanke shawarar kirkirar wani zaure (Goup) a facebook, wanda duk rubutun da muka juya na wadancan takardun, za mu rika tura (posting) su a cikin zauren har zuwa lokacin da muka gama juya su gaba daya. Mun kiyasta aikin zai kai mu shekara daya. Duk wanda yake da sha'awar shiga wancan zauren zai ajiye kudin rijista, wanda da kudin ne za mu rage wasu ayyuka na buga littafin.
A baya, mun kasa rijistar kamar haka:
Wata daya a cikin zauren N1,000
Wata biyu N2,000
Wata uku N2,500 (amma a jere)
Wata shida N5,000 (shi ma a jere)
Shekara daya N10,000
Sa'annan idan an kammala aikin littafin, wadanda suka yi rijista su ne za su fara samun littafin da rangwamen farashi gwargwadon rijistar kowa. Idan ta N1,000 aka yi za a sami ragin 10%, ta N2,000 kuma 20%, ta N5,000 kuma 50%. Idan aka yi ta shekara watau N10 000 za a sami ragin 100%, watau za a sami duka littattafan kyauta.
To, amma yanzu ga yadda sabon tsarin yake:
Bisa la'akari da koke-koke da kuma korafin mutane da dama, sannan kuma da la'akari da halin rashi da mafi yawancin 'yan kasar nan suke ciki, mun yanke shawarar mayar da rijistar shiga ZAURUKAN sau daya har zuwa lokacin gama karatun littafin gaba daya. Dangane da haka ga sababbin tsare-tsaren shiga ZAURUKAN DARE DUBU DA DAYA da aka amince da su.
1. Duk wanda zai shiga ZAURUKAN zai biya kudin rijista ta Naira DUBU DAYA (N1000) ne kacal har a gama karanta duka littafin.
2. Wannan kudin rijista na N1,000 na karatu ne kawai a facebook, bai shafi mallakar kwafin littattafan ba idan sun fita kasuwa.
3. Idan ana bukatar kwafin littattafan, to, tsohon tsarin rijista yana nan. Watau za a biya Naira dubu goma (N10, 000), kuma za a ci gaba da biya sannu a hankali har a ajiye kudin kafin kammala aikin littattafan.
4. Idan kuma an fara biyan kudin kwafin littattafan sai wata matsala ta sa mutum bai cika kudinsa ba, to, zai sami rangwame gwargwadon kudin da ya ajiye (idan ya ajiye 2,000 ne zai sami rangwamen 20%. Idan 5,000 ne zai sami rangwamen 50%) kamar dai yadda tsohon tsarin yake.
5. Duk wadanda suka rigaya suka yi rijista ta tsohon tsari, watau watan Disamba da Janairu, to, za a cire Naira dubu 1,000 a matsayin kudin rijista na gaba dayan shekarar, abin da ya yi saura na daga kudinsu, sun zama zubi a kan mallakar kwafin littattafan idan an gama aikinsu.
Misali:
I. Wanda ya yi rijista ta wata daya, N1000 ya biya kudin rejista kenan baki daya har a gama karatun littattafan. Idan yana bukatar kwafin littattafan kuma zai iya ci gaba da zuba kudin har ya tunfaye sauran N9,000. Idan kuma bai da bukatar mallakar kwafin, to, shi ke nan.
II. Wanda ya biya kudin rijistar wata uku, N2500, za a cire N1000 na sabon tsarin rijista, sauran kudi, N1500 sun zama zubi. Zai iyar da cika N8,500 domin mallakar kwafi, idan kuma bai da dama, har aka gama aikin littafin bai cika ba, to, zai sami ragi na 20%.
III. Wanda ya yi rijistar wata shida, N5,000, za a cire N1000 na sabon tsarin rijista, saura N4,000 sun zama zubi na kwafin littafi. Sai ya cika N6000 domin mallakar littafin kyauta. Idan kuma bai sami halin cikawa ba zai sami ragi na 50%.
IV. Wadanda suka yi rejista ta shekara kuwa, N10,000, to, kwafin littattafan kawai suke jira Idan an kammala karatu da aikin littafin.
6. A halin yanzu, duk wadanda suka rigaya suka yi rijista, kuma suke cikin zauren na DARE DUBU DA DAYA, ba ya da bukatar sabunta rijista, kamar yadda tsohon tsarin ya tanadar, har mu kammala karatu, sai dai a yi kokarin ajiye kudin mallakar kwafin littafin. Zuwa yanzu mun sami mutane da dama da suka yi rijista.
Ko da rijista, ko babu, mu dai mun sha alwashi sai mun juya wannan rubutun hannu zuwa rubutun computer, sannan duk yadda za a yi sai mun samar da cikakken wannan littafi ga al'ummar Hausawa, kamar yadda wasu harsunan duniya suka fassara shi ga al'ummarsu. Idan ba a sami yin rijista ba, to a taimaka mana da addu'a, domin ganin mun iyar da aikin da kakanninmu suka faro tun shekara dari da suka wuce. Sannan sai a jira fitowar littattafan a kasuwa, nan da shekara daya, In Sha Allah.
GA YADDA ZA A BIYA KUDIN RIJISTA:
• Ga wadanda za su biya a banki ga asusun ajiyar da za a tura kudin rejista kamar haka:
* Bankin UNITY:
SUNA: Ibrahim Malumfashi,
Lambar asusu: 0018960303.
* Bankin UBA:
SUNA: Ibrahim Malumfashi,
Lambar asusu: 2018484292.
* Bankin UBA: (Domin wadanda ke kasashen
waje)
SUNA: Ibrahim Malumfashi,
Lambar asusu: 0131000465
Ana kuma iya sayen katin waya na adadin kudin rijistar da za a yi, sai a tura wa wannan lambar 08066699976 (amma katin MTN kawai). Idan za a tura katin sai a hada da sunan da ake amfani da shi a facebook, domin mu san wanda ya turo.
KARIN BAYANI
Idan muka yi la'akari da littattai biyar da NNPC suka buga daga fayil guda, kudinsu ya kama N2,500. To, da za a ce littattafan nan biyar sun zama littafi guda (daga fayil guda) a yi sauran fayilolin sha hudu, to, nawa kudin littattafan gaba daya za su kama idan aka buga dukkan fayilolin gama sha hudu? Kenan za su kama; N2,500 x 14 = N35,000.
To, amma mu, ga shi za mu buga dukkansu a N10,000 kacal. Amma fa wannan garabasar ga wadanda suka yi rijista ne kawai. Wadanda ba su yi ba, za su saye shi daidai farashin da kowa zai saye a kasuwa.
Domin karin bayani kai waye, ko kuma idan an biya kudin rijista, sai a tuntubi daya daga cikin wadannan mutane:
1. Farfesa Ibrahim Malumfashi
Phone: 08035924022
Email: mfashi@yahoo.com
Facebook: http://facebook.com/malumfashii
2. Bukar Mada
Phone: 08021218337
Email: bukarmada@gmail.com
Facebook: http://facebook.com/bukarmada
3. Danladi Haruna
Phone: 08030764060
Email: dharuna@gmail.com
Facebook: http://facebook.com/dharuna
ALLAH YA YI MANA JAGORA.
DA MUGUN SARKI....
Suna nan haka sai wasu daga cikinsu suka ce, ina amfanin zamanmu haka babu wani Sarki da zai rika mulkinmu, ba mu da wasu dokoki da za su tafiyar da tsarin rayuwarmu. Allah kuwa ya amshi addu'arsu!
Ana nan wata rana sai wani dan guntun reshen bishiyar da take bakin tabkin ya karye, ya fado kwatsam a gefen tabkin. Kwadi suka tsorata suka fada ruwa da gudu. Sai wasu daga cikinsu suka ce ai Sarkin da suke roko a turo musu ne Allah ya turo musu.
Kwadi na cikin ruwa suna jira su ji irin dokokin da Sarki zai shata musu, suka ji shiru, su kuma suna jin tsoron su matsa kusa da shi. Ana nan dai har wani mai karfin hali daga cikinsu ya matsa kusa da reshen itacen nan da ya fado, sannu-sannu har ya kai ga taba shi, icce bai motsa ba, har ya hau kansa, yana rawa, itace dai bai motsa ba. Da saura suka ga haka, sai duk suka fito suka haye kan reshen itace. Sai ya kasance koyaushe nan ne wurin zaman kwadi tare da sabon Sarkinsu.
Sai dai kwadi ba su yi murna da wannan Sarki da aka turo musu ba, suka nuna sun fi son Sarki mai rai, mai motsi, wanda zai rika shata musu dokoki, kuma ya shimfida mulkinsa.
Wannan buri na kwadi ya sa Allah ya yi fushi da su. Kwaram ran nan sai ga wani zalbe zai wuce ta wurin, sai ya ga kwadi da yawa bakin tabki, shi ke nan abin nema ya samu, dama wurin neman abinci zai tafi. Sai ya tsaya bakin tabkin nan ya rika kama kwadi yana cinyewa.
Da kwadi suka ga zalbe ya dame su da kisa haka, ya hana su sakat, sai suka ce wannan wane irin Sarki ne aka turo mana. Mu dai mun fi son zamanmu na da. DA MULKIN ZALUNCI GWAMMA ZAMA BABU SARKI!







