Thursday, May 11, 2017

TARIHIN FULANI: Nasabar Toronkawa.

(Daga Littafin Tarihin Fulani na Wazirin Sokoto wanda kamfanin ɗab'i na NNPC ya wallafa a shekarar 1956)
#Sadiq Tukur Gwarzo



Ana ce Musu Toronkawa ne saboda sun zauna a kasar Toro. Ita Toro Kasa ce a can yamma maso kudu na Afirka ta yamma. Sun taso ne daga wajajen 'ɗurisina' cikin kasar Sham (syria), sun biyo daga gefen arewa ta Afirka ta yamma har suka sadu da Toro suka Zamna wurin.

     Suka yi  yawa kwarrai, har lokacin da aka aiki ukubatu yaki Afirka, ya sadu dasu. Sai suka shiga addinin islama ba tare da anyi faɗa ba. Ukubatu ya auri ɗiyar Sarkinsu, sunanta Bajju Mangu. To su Toronkawa jinsi ne da suka fito daga zuriyar Ramo, ɗan Isa, ɗan Ishaku, ɗan Annabi Ibrahim (AS).

    Bajju Mango ta haifi ɗiya huɗu da ukubatu, sune:- 1. Delta 2. Woya 3. Roruba da 4. Nasi.
   Waɗannan sune asalin dukkan fulani da suka fara magana da fulatanci.

Toronkawan dauri, harshensu wakuru ne.
Daga baya zuriyar Ukbatu ta yawaita.

1. Daga ɗiyan Delta kabilar songhay ta fita.

2. Daga ɗiyan Nasi dangin ba'awina da wolorɓe suka fita.

3. Daga ɗiyan Woya dangin Furɓe suka fita

4. Daga ɗiyan Rorube dangin woloɓe suka fita.

   Bayan sunyi yawa, sun zauna a wuri mai suna Falgu, sai suka rabu da sauran Toronkawa na Futa-Turo.

   Lokacin da sukayi karfi, sai suka ɗauki yaki babba. Suka tasar ma Futa sukaci amanar Sarkin Futa suka kasheshi yana sallar Idi. Suka kama kasar futa suka zauna suna ɓarnace-ɓarnace.

   Sannan sai wani malami daga cikin Toronkawa ya tashi yayi Jihadi dasu, ya rinjayesu, ya gyara kasa ya zuba adalci, ya kyautata zaman toronkawa.

  To bayan Rasuwarsa sai Fulani Jinin Ukubatu suka sake kawo yaki ga Toronkawa, suka koresu daga Futaƴ, suka sake kama kasa tare da shiga ɓannace-ɓannace.

   Bayan haka kuma sai fulani Toronkawa sukayi shirin yaki da Fulani jikokin Ukubatu, suka taho da yaki, sukayi faɗa dasu mai tsanani har suka rinjayesu mugunyar rinjaya. Saboda haka sai fulani ɗiyan ukubatu suka kasu uku.

- Kashi ɗaya suka saduda sukabi Toronkawa

- Kashi na biyu suka koma Falgu inda suka soma zama da fari

- kashi na uku suka yo gabas suka tsammaci zasu riski 'yanuwansu Larabawa saboda Ubansu balarabe ne. Wasu cikinsu sun iya komawa kasar larabawa, wasunsu kuma sun kasa basu karasa ba. Sunan babban su Dunurundi.

  To waɗannan da basu karasa ɗinba, daga cikin sune zuriyar Beni yalalɓe, da sissilɓe, da walanɓe, da gumborawa da gwalankwa'en da fulanin Adamawa suka fito.

   Waɗannan sune dangogin da suke daga cikin zuriyar da suka taho daga Naskanga tare da Dunurundi.

  Su waɗancan sunfi toronkawa yawa. Domin an samu kashin farko da suka koma Falgo daga baya sun kara kawowa Toro yaki suka cinyeta tare da sake komawa ɓarna, har sai da aka samu wani daga toronkawa mai suna Sulaiman yayi yaki dasu ya koresu ya watsasu, ya naɗa sarki Abdulkadir. Bayansa kuma sai anka naɗa Muhammadul Amin, anka zamna lafiya, Toronkawa suka amince da filani ɗiyan ukubatu.

  Bayan waɗannan al'amura da muka faɗa, lokacin nan Musa Jakollo kakan Shehu Usmanu ya taso da jama'arsa don gudun fitina, ya fuskanci gabas har ya karaso 'K'wanni' a shekara ta 500AH. Shikuma ɗiya nai sai suka warwatsu. Kaso ɗaya sune ɗiyan Ali, na biyu ɗiyan ɓininga, sai ɗiyan Kogga, sai ɗiyan ɓaleni da ɗiyan Raneni. Diyan ɓininga ne suka tashi daga kwanni sa'ar da Sarkin kwanni Damka ya zambace su ya karkashe su, ya kama ɗiyansu ya yasashe dukiyar su. Diyan Ali sun sauka a wani wuri da ake kira Kuluba.

   DANGANTAKAR SHEHU ZUWA MUSA JOKOLLO

Abinda ma'anar fodio shine Malami, kuma wanda malami ya haifa. Shine Fodio ɗan Usmanu ɗan Salihu, ɗan Haruna ɗan Muhammadu Gurɗo ɗan Jaɓɓo ɗan Mamman Samba ɗan Masirana ɗan Ayuba ɗan Baba fan Abubakar ɗan Musa Jakolli wanda yake da ɗiyan Imamu Demba. Intaha.

   Idan har Ingancin wannan Tarihin ya tabbata, muna iya kallonsa a matsayin sabuwar fuska saɓanin wanda ake yaɗawa mai cewa Fodio Aljana ce kuma itace ta haifi shehu Usmanu.. Koda Yake, har yanzu na lura dacewa Fulani da yawa suna ji a ransu cewar Asalinsu gamin gambiza ne tsakanin Larabawa da Aljannu.

    Watakila dai, abinda yake akanmu bai wuce binciko tarihin silsila ko ace rarrabuwar kabilun fulanin ba, kamar misalin Sulluɓawa, Danejawa, Natirawa, Agalawa, Holma, Bongwa, Naturɓe, Ba'awa (anfaɗi silsilar su a sama), Rudunnawa, Magawa da dai sauransu.

(c) 2017 Taskar Hikayoyi

No comments:

Post a Comment