Monday, July 7, 2014

DARE DUBU DA DAYA

CIKAKKEN BAYANI GAME DA RIJISTAR SHIGA ZAUREN DARE DUBU DA DAYA.

Amincin Allah ya tabbata a gare ku.

Ganin yadda jama'a suke ta nuna sha'awarsu game da hikayoyin wannan littafi na Alfu Laila wa Lailatun ko kuma DARE DUBU DA DAYA, shi ya sa ni (Bukar Mada), da Professor Ibrahim Malumfashi, da wani marubuci mai suna Danladi Haruna, muka yanke shawarar samar da cikakken wannan littafi (tun daga dare na 1 har zuwa Dare na 1001) da Hausa domin al'ummar Hausawa su sami abin karantawa.

Littafin DARE DUBU DA DAYA shahararen littafi ne na Larabawa da ya yi fice a fadin duniya gaba daya. An fassara shi cikin harsunan duniya da yawa, ciki har da Hausa. Na hausar an fassara shi fiye da shekara dari (100) da suka wuce, lokacin babu Typewriter ko computer a kasar Hausa, wani bature ne mai suna Frank Edgar ya rubuta tare da taimakon wasu Malamai na kasar Sokoto, don haka da hannu aka yi rubutun (kamar yadda kuka ga samfur din rubutun a cikin wannan hoto).

Rubutun na nan a cikin taskar ajiyar tsofaffin bayanai na Kaduna, fayil goma sha hudu (14). Kowane fayil akwai takarda 700 zuwa 800 ciki. Shi ne Kamfanin NNPC suka buga littafi biyar daga fayil na farko (duk littafi daya na NNPC ana sayar da shi N500 ne a kasuwa, idan kuka hada littafi biyar, watau fayil guda kenan, kudinsu ya kama N2,500). Sauran fayilolin ba a kuma kula su ba, balle a buga su, su zama littattafai.

Ganinirin muhimmancin aikin a Adabin duniya shi ne muke wannan yunkurin yanzu na ganin mun juya wannan rubutun hannu, na dukkan fayilolin 14, zuwa rubutun computer, sannan mu buga littattafan don sayarwa ga al'umma. Hoto (photocoy) kawai na takardun da muka yi, sun lashe kudi sama da dubu saba'in(N70,000). Kenan wannan ba karamin aiki ba ne, sai an nemi gudummawa ga jama'a.

Daga nan sai muka yanke shawarar kirkirar wani zaure (Goup) a facebook, wanda duk rubutun da muka juya na wadancan takardun, za mu rika tura (posting) su a cikin zauren har zuwa lokacin da muka gama juya su gaba daya. Mun kiyasta aikin zai kai mu shekara daya. Duk wanda yake da sha'awar shiga wancan zauren zai ajiye kudin rijista, wanda da kudin ne za mu rage wasu ayyuka na buga littafin.

A baya, mun kasa rijistar kamar haka:

Wata daya a cikin zauren N1,000
Wata biyu N2,000
Wata uku N2,500 (amma a jere)
Wata shida N5,000 (shi ma a jere)
Shekara daya N10,000

Sa'annan idan an kammala aikin littafin, wadanda suka yi rijista su ne za su fara samun littafin da rangwamen farashi gwargwadon rijistar kowa. Idan ta N1,000 aka yi za a sami ragin 10%, ta N2,000 kuma 20%, ta N5,000 kuma 50%. Idan aka yi ta shekara watau N10 000 za a sami ragin 100%, watau za a sami duka littattafan kyauta.

To, amma yanzu ga yadda sabon tsarin yake:

Bisa la'akari da koke-koke da kuma korafin mutane da dama, sannan kuma da la'akari da halin rashi da mafi yawancin 'yan kasar nan suke ciki, mun yanke shawarar mayar da rijistar shiga ZAURUKAN sau daya har zuwa lokacin gama karatun littafin gaba daya. Dangane da haka ga sababbin tsare-tsaren shiga ZAURUKAN DARE DUBU DA DAYA da aka amince da su.

1. Duk wanda zai shiga ZAURUKAN zai biya kudin rijista ta Naira DUBU DAYA (N1000) ne kacal har a gama karanta duka littafin.

2. Wannan kudin rijista na N1,000 na karatu ne kawai a facebook, bai shafi mallakar kwafin littattafan ba idan sun fita kasuwa.

3. Idan ana bukatar kwafin littattafan, to, tsohon tsarin rijista yana nan. Watau za a biya Naira dubu goma (N10, 000), kuma za a ci gaba da biya sannu a hankali har a ajiye kudin kafin kammala aikin littattafan.

4. Idan kuma an fara biyan kudin kwafin littattafan sai wata matsala ta sa mutum bai cika kudinsa ba, to, zai sami rangwame gwargwadon kudin da ya ajiye (idan ya ajiye 2,000 ne zai sami rangwamen 20%. Idan 5,000 ne zai sami rangwamen 50%) kamar dai yadda tsohon tsarin yake.

5. Duk wadanda suka rigaya suka yi rijista ta tsohon tsari, watau watan Disamba da Janairu, to, za a cire Naira dubu 1,000 a matsayin kudin rijista na gaba dayan shekarar, abin da ya yi saura na daga kudinsu, sun zama zubi a kan mallakar kwafin littattafan idan an gama aikinsu.

Misali:

I. Wanda ya yi rijista ta wata daya, N1000 ya biya kudin rejista kenan baki daya har a gama karatun littattafan. Idan yana bukatar kwafin littattafan kuma zai iya ci gaba da zuba kudin har ya tunfaye sauran N9,000. Idan kuma bai da bukatar mallakar kwafin, to, shi ke nan.

II. Wanda ya biya kudin rijistar wata uku, N2500, za a cire N1000 na sabon tsarin rijista, sauran kudi, N1500 sun zama zubi. Zai iyar da cika N8,500 domin mallakar kwafi, idan kuma bai da dama, har aka gama aikin littafin bai cika ba, to, zai sami ragi na 20%.

III. Wanda ya yi rijistar wata shida, N5,000, za a cire N1000 na sabon tsarin rijista, saura N4,000 sun zama zubi na kwafin littafi. Sai ya cika N6000 domin mallakar littafin kyauta. Idan kuma bai sami halin cikawa ba zai sami ragi na 50%.

IV. Wadanda suka yi rejista ta shekara kuwa, N10,000, to, kwafin littattafan kawai suke jira Idan an kammala karatu da aikin littafin.

6. A halin yanzu, duk wadanda suka rigaya suka yi rijista, kuma suke cikin zauren na DARE DUBU DA DAYA, ba ya da bukatar sabunta rijista, kamar yadda tsohon tsarin ya tanadar, har mu kammala karatu, sai dai a yi kokarin ajiye kudin mallakar kwafin littafin. Zuwa yanzu mun sami mutane da dama da suka yi rijista.

Ko da rijista, ko babu, mu dai mun sha alwashi sai mun juya wannan rubutun hannu zuwa rubutun computer, sannan duk yadda za a yi sai mun samar da cikakken wannan littafi ga al'ummar Hausawa, kamar yadda wasu harsunan duniya suka fassara shi ga al'ummarsu. Idan ba a sami yin rijista ba, to a taimaka mana da addu'a, domin ganin mun iyar da aikin da kakanninmu suka faro tun shekara dari da suka wuce. Sannan sai a jira fitowar littattafan a kasuwa, nan da shekara daya, In Sha Allah.

GA YADDA ZA A BIYA KUDIN RIJISTA:

• Ga wadanda za su biya a banki ga asusun ajiyar da za a tura kudin rejista kamar haka:

* Bankin UNITY:
SUNA: Ibrahim Malumfashi,
Lambar asusu: 0018960303.

* Bankin UBA:
SUNA: Ibrahim Malumfashi,
Lambar asusu: 2018484292.

* Bankin UBA: (Domin wadanda ke kasashen
waje)
SUNA: Ibrahim Malumfashi,
Lambar asusu: 0131000465

Ana kuma iya sayen katin waya na adadin kudin rijistar da za a yi, sai a tura wa wannan lambar 08066699976 (amma katin MTN kawai). Idan za a tura katin sai a hada da sunan da ake amfani da shi a facebook, domin mu san wanda ya turo.

KARIN BAYANI

Idan muka yi la'akari da littattai biyar da NNPC suka buga daga fayil guda, kudinsu ya kama N2,500. To, da za a ce littattafan nan biyar sun zama littafi guda (daga fayil guda) a yi sauran fayilolin sha hudu, to, nawa kudin littattafan gaba daya za su kama idan aka buga dukkan fayilolin gama sha hudu? Kenan za su kama; N2,500 x 14 = N35,000.

To, amma mu, ga shi za mu buga dukkansu a N10,000 kacal. Amma fa wannan garabasar ga wadanda suka yi rijista ne kawai. Wadanda ba su yi ba, za su saye shi daidai farashin da kowa zai saye a kasuwa.

Domin karin bayani kai waye, ko kuma idan an biya kudin rijista, sai a tuntubi daya daga cikin wadannan mutane:

1. Farfesa Ibrahim Malumfashi
Phone: 08035924022
Email: mfashi@yahoo.com
Facebook: http://facebook.com/malumfashii

2. Bukar Mada
Phone: 08021218337
Email: bukarmada@gmail.com
Facebook: http://facebook.com/bukarmada

3. Danladi Haruna
Phone: 08030764060
Email: dharuna@gmail.com
Facebook: http://facebook.com/dharuna

ALLAH YA YI MANA JAGORA.

3 comments:

  1. Wannan tsari ya yi. Allah ya taimaka.

    ReplyDelete
  2. Gaskiya yayi sede akwai 'yan tambayoyin danake dasu kamar haka
    dafarko, misali kaman yanzu na bukace na kwafi in bayan angama sarrafa wa kenan wato na 10,000, to muda muke nisa daku tayaya za'ayi mu mallakeshi a hannunmu??? Sannan kuma in mutum ya subscribe na 1000 wato na month shin da adinga zubo labarin littattafan ta facebuk ne kokuwa tawani bangare na daban??? dafatan zan samu amsa so shina dawuri, Allah yatemake mu, kuma Allah yabamu tsahon rai harsanda za'aga ma kammala wannan littafin ....ameen

    ReplyDelete
  3. Allah ya taimake ku ya baku jajircewa a kan wannan aiki.

    ReplyDelete