Sunday, May 14, 2017

NAZARI KAN ASALIN HAUSA

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
    08060869978

Kashi na ɗaya

Gabatarwa

Da Sunan Allah mai Rahama mai jinkai.
   A ɗaukacin tsoffin biranen kasar hausa, kukoki nanan burjuk a inda akasari ya zamo gonaki a yanzu. A wasu tsoffin biranen duniya, tsoffin gine-gine da tsoffin masana'antu, ko kaburbura ke nuna rayuwa ta wanzu a waɗannan wuraren. 

    Idan har Kukoki ne kaɗai babbar shaidar da zamu iya gane cewa rayuwar hausawa ta taɓa wanzuwa shekaru da dama da suka gabata a wani wuri saboda kila tun asali hausawa basa manyan gidaje da kere-kere waɗanda buraguzansu zasu samu tsira har zuwa yanzu, to ya kamata muyi nazarin labarun da waɗannan kokuki tsofaffi suke bayyanawa a garemu.
    A kabilar Nkwici ta Kasar Malawi, ana kiran bishiyar Kuka da sunan 'Bishiyar Rayuwa'. Saboda a cewar su, bishiyar na baiwa mazauna kauyuka mafaka a zamanin yaki yayin da mahara suka nufosu. Sannan ana amfani da ganyenta da kuma 'ya'yanta don abinci gami da magani. Har ila yau, akwai canfe-canfe da dama a tattare da ita.
   A kasar Madagaskar kuwa, an samu wata gagarumar Bishiyar kuka mai kimanin shekaru dubu uku, tsayinta zai tasamma kafa ɗari, faɗin ta kuwa an kiyasta sai mutane akalla goma sun kama hannuwan juna zasu iya rutsata. Mutanen yankin suna matukar girmama wannan kukar, har suna kiranta da 'Bishiyar Mutuwa', domin anasu fahimtar, duk wanda ya mutu a yankin, nan ruhinsa ke zuwa ya zauna.
   A gundumar Linpopo dake South Africa, an samu wata gagarumar Bishiyar kuka. Tsayinta da faɗinta duk sun haura kafa talatin da biyar kowanne. Tana da kogo, wanda aka ayyana cewar mutane acan baya sun maida kogon wajen fira ko wajen fakewa, domin an samu wasu abubuwa irin na sojin-da da kuma na mu'amala aciki, binciken 'carbon dating' na masana kimiyyar zamani ya kiyasta cewar bishiyar takai kusan kimanin shekaru dubu shida a raye.
   Akwai kuma sirrin kuka da Marubuci ɗan kasar faransa Richard Mabey ya ruwaito a littafinsa mai suna 'The Caberat of Plant' cewar Giwaye da manyan namun daji suna zuwa jikin kuka susha ruwa. Wai da zarar sun hangota alhali suna cikin ɗimuwar kishi, sai aga sun nufeta da gaggawa, sannan su yage bayanta su soma lasa. ƊDaga bisani bincike ya nuna cewa bishiyar na iya tanajin ruwa sama da lita dubu ɗari gwargwadon girmanta da adadin shekarunta.
    Idan waɗannan abubuwan da mukaji daga Sassan duniya gaskiya ne, shin me muka samu game da kuka a kasar hausa? Kpɓkuma wane labari kokokin kasar hausa suke bamu?
   Irin waɗancan manyan kukoki nanan barbaje a kasar hausa. Wasu ma an lakaba musu sunaye mabanbanta, watakila na mutanen da sukafi zama a karkashin kukokin ne. Misali, akwai Kukar Boka, Kukar Gajere, Kukar kwanɗi.. Da sauransu.
   A bisa tsoffin hausawa da fulani da muka tambaya, kusan ɗaukacin su sun tafi akan cewa duk kukar daka gani da kanta ta fito ba shukata akayi ba. Wannan fa ana magana ne akan matasan kukoki waɗanda muke ganin basu tara shekaru da dama ba, amma game da manyan kukoki masu alamar shekaru, Tsoffin sun tabbatar mana da cewa tasowa sukayi suka gansu.
   Haka nan, ana iya lura cewar a gonaki da dazuzzuka inda babu mutane dake rayuwa a wurin, ba kasafai bishiyar kuka ke fitowa ba. Amma kuma mafi yawan unguwannin hausa na tsofgin garuruwa na ɗauke da bishiyar kokoki. A wani sa'in ma, akan samu bishiyar kuka a kowanne gida, ko kuma a bayan gidan.
  Watakila, hakan na nuna cewar sai da mutane suka fara zama a wannan wuri sannan kukokin suka fito. Idan kuwa hakan ta tabbata, to zamu iya sanin shekarun kukoki a kasar hausa ta hanyar binciken zamani, sannan da watakila zamu iya sanin jimawar lokacin da hausawa suka fara zama a wannan wuri, tayadda daga bisani zamu gane gari mafi tsufa a kasar hausa.
   Idan kuma ta tabbata cewar yawan bishiyoyin kuka ke nuni da yawan mutanen da suka rayu a gari, da shima zai zamo mana ma'auni mafi sauki don gane tsoffin garuruwan da sukafi tumbatsa da mutane shekaru aru-aru da suka wuce..

Za mu ci gaba...

(c) 2017 Taskar Hikayoyi

No comments:

Post a Comment