Friday, May 19, 2017

NAZARI KAN ASALIN HAUSA

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
    08060869978

Kashi na uku

Farfesa Umar El zakzaky Al Bahaushe yace" kwayoyin halittar Fir'auna Seti, wannan daya yayyanka yahudawan zamaninsa, da kuma na magajinsa Fira'una Remesis II, wanda yayi zamani da Annabi Musa A.S sunyi kamanceceniya da kwayoyin halittar mutanen kano na yau, musamman ma nacikin kwaryar badala."


   Sai dai Farfesa Muzzah Jibrin, Farfesa Abdullahi Elkanawy da wasu masana da dama sunyi watsi da wannan bincike. Ga abinda ya fito daga makalar masanan kamar yadda suka gabatar a wani taro daya gudana a Arewa House dake kaduna:
   Kuskure ne a hada asalin wancan Fir'aunan da kano tunda Gawar Mornoptah, dan Fir'auna Remeses II, fir'aunan da aka halakar a ambaliyar ruwa yayin da yake bin sawun Annabi Musa A.S don ya halaka shi, wadda Masani Loret ya gano a shekarar 1898 a tsohon birnin Thebes ta nuna cewar kwayoyin halittar ta sunfi kamanceceniya dana mutanen egypt ne ba mutanen kano ba".
  A wani kaulin kuma, masanan sunyi hasashen cewa kwayoyin halittar mutanen zariya dana kabilar Gwari da Igala suma sunyi kamanceceniya da juna, wanda hakan na nuni da cewar kodai kabilun asalinsu a zariya suke da zama, ko kuma al'ummar kabilun ne suka kafa garin na zaria lokaci mai tsawo daya shige, don haka yanuwan juna ne kenan. Muna kuma iya cewa daga jikin mutum guda kabilun suka fita.
   Amma maganar su da sukace sun auna wasu ɓuraguzai na kasusuwan mutanen dake kwance a wasu makabartu a kano, har kuma sun gano cewar mafi yawan kwayoyin halittar mutanen kano yafi nuni dana Sharifai, kamar akwai siyasa a ciki.
   Tabbas, tarihi ya nuna cewar a wajajen karni na goma sha uku, wangarawa karkashin Sheik Abdurrahman Zaiti tare da wasu malamai kimanin arbain irinsu Modibbo sheshe, Mandawari, Limamin Madatai, Limamin Jujin 'yan labo sunzo kano har ma suka kawo musulunci garin. Lokacin Sarkin Kano Yaji dan Tsamiya ke bisa gadon sarauta.
   Sai kuma a karni na goma sha biyar zamanin Sarkin Kano Rumfa Akace wani balarabe masani mai suna Imam Maghili ya ziyarci kano shima da wasu jama'a tasa. Daga baya ma ance yabar wasu daga zuriyarsa anan kano, wadanda su ake kira Sharifai zuwa yanzu.
   Marubuci, marigayi Maje Ahmad Gwangwazo ya kawo wata muhimmiyar gaba a shafi na 22 na littafinsa mai suna Wangarawa Sun iso Kano, inda yake cewa "Sheik Abdullahi Ilorin ya nuna cewar tun a karni na goma sha ɗaya wangarawa suka fara bazuwa suna yaɗa musulumci a afirka ta yamma. Yace su wangarawa kasarsu ta farko misira(Egypt). Yace asalin mazaunan kabilar Sundiata da asalin kabilar Kakan Mansa Musa da asalin kabilar Songhai irinsu Askiya Muhammad kenam, tarihi ya nuna duk a misira suke kafin su iso Mali, inda mafi yawan masu tarihi ke cewa daga Mali wangarawa sukazo, amma Mali din
ma zuwa sukayi".
   Sai dai, koda auratayya ta wanzu tsakanin wangarawa da larabawan da suka sauka a kano da kanawa bakaken fata na lokacin, da wuya ace an samu kwayoyin halitta sunyi irin wannan mamakon rinjayar. Domin kuwa  kano tun asali garin bakaken fata ne ba farare ba, ba kuma a taɓa samun cewar an maye mutanen kano da wasu mutanen ba, don haka faɗin cewar kwayoyin halittar kanawa ya nuna su sharifai ne ba lalle ya zamo ya inganta ba.
   Amma tana iya yiwuwa, anyi rashin sa'a, ɓuraguzan da aka samu a makabartun waɗanda akayi wannan gwajin dasu (sample) na Wangarawa da larabawan ne dana zuriyarsu wadanda watakila sun cakuɗu da bakaken fata, don haka binciken bai iya bada labarin ɗaukacin mutanen kano ba, tunda dokar irin wannan binciken ta nuna cewa wajibi ne abubuwan da za'ayi bincike akansa su zamo suna wakiltar ɗaukacin abinda ake magana akansa.
   Wani abin lura ma anan shine shigar siyasar addini acikin dukkan binciken.
  Munji bincike na farko ya nuna cewar Fir'aunan daya kashe jarirai ɗan kano ne, don haka wasu ke ganin hakan kamar kaskanci ne ga kanawa, shiyasa sukuma suka wanke kanawa da cewar asalinsu sharifai (jikokin fiyayyen halitta) ne..
   A hakika dai, bamu da karan nunawa ga waɗancan Malumma masu girma, amma wajibin mune mu karɓi gaskiya komai ɗacinta dangane da asalin mu. Maganar addini ba zata sa mu ɓoye asalin muba, tunda da ayyukan mu akace za'ay mana hisabi bada asalin muba. Rashin ingancin binciken na farko shine kurum hujjar da zatasa muki aminta dashi amma ba laifiɓ da firaunan ya aikata ba.
   Akwai binciken masana dake cewa Kwayoyin halittun Firauna Remesis II yafi kamanceceniya da kwayoyin halittun mutanen Afirka ta tsakiya a ma'auni na farko, daga nan sai mutanen kasar south Africa a ma'auni na biyu, sannan mutanen Afirka ta yamma inda hausawa suke a ma'auni na uku. Wanda hakan ke nuna alakar hausawa da wancan firauna tayi tazara da shekaru masu nisan gaske... (Watakila sai kowacce kabila daga cikin biyun ta tike da Annabi Nuhu ko Annabi Adamu za'a ɗiga aya)
  Sai dai kuma, akwai tsohon zance dake nuna kwararowar misirawa izuwa yankin afirka ta yamma a tsahon zamani daya shuɗe. Watakila tun zamanin Annabi Musa A.S hakan ta faru, ko kuma wani lokaci kafin haka, domin kuwa labarin baka yana nuna cewar garin Auyo dake jihar jigawa  ya kafu tun kafin Haihuwar Annabi Musa A.S, sai dai kuma karancin tarihin da muke dashi akan kabilar Auyokawa da akace sune suka kafa garin ke hanamu gane alaka ta jini ko ta sadarwa da wayewa a tsakanin mutan garin da kuma misira tun a wancan tsohon zamani.
  Da alama dai, Magana mafi inganci bisa kwayoyin halittar hausawa shine wanda wasu gungun masana suka gudanar akan hausawa mazauna sudan.
   Da fari, Binciken ya nuna cewar kashi arbain na kwayoyin halittun hausawa dake zaune a sudan sunyi dai-dai dana kabilun sudan ɗin. (Hassan et al 2008)
   Akwai kuma makamancin binciken daya nuna cewa kwayoyin halittar Hausawa ya nuna cewa su 'yanuwan juna ne da wasu kabilu masu amfani da yaren Nilu mazauna Nigeria, Cameroon, Central Chad da kuma kudancin Sudan. (Toshkoff et al 2009).
  Binciken ya nuna cewar asalin yaren hausa, da yarukan waɗancan kabilu guda ɗaya ne saboda alakar yarukan da aka gani suna dashi da juna.
   Bakaken fatar chadi dana kamaru duk ana tsammanin sun gangara yankin ne shekaru da dama da suka gabata daga daular sudan. Sukuwa mazauna sudan, duk da gaurayuwar kwayoyin halittun larabawa dana sauran kabilu a tattare dasu, an gamsu da cewa su jikokin tsoffin bakaken fata ne na tsohuwar daular nan ta 'Meroa' data shahara a duniya wadda ta wanzu a sudan ɗin.
   Ta haka, sai ake hasashen cewa kakannin hausawa da kakannin sudawa da kakannin wadancan kabilu mazauna cameroon da chadi sun fito ne daga tsatson Uba daya, amma hijirar data rinka aukuwa tsakankanin mutanen_da shine sanadiyar rarrabuwarsu ta yadda yanzu kowa yayi nesa da kowa. Hasashen kuma na nuna cewar wannan rarrabuwa ta auku akalla da shekaru dubu biyu baya zuwa sama, tayadda a iya wancan lokacin ne kowacce kabila tayi chakuduwa da sauran kabilu har kashi sittin na kwayoyin halittar su ya sauya, kashi arbain ne kadai zuwa yanzu bai jirwaya ba. Babbar hujjar hakan itace  samuwar wasu kabilun daga jikin waɗancan na ainihi, tayadda ansan ana ɗaukar tsawon lokaci kafin faruwar hakan. Sai kuma tsawon zamanin da daular bakaken fatar tayi a raye har kuma ta rushe. Kamar abinda Marubuci Morton H. Fried ya faɗa a littafinsa mai suna 'The Notion of the Tribe' cewar akwai kabilu na ainihi (primary tribe), akwai kuma kabilu samammu daga na ainihi (secondary tribe).
    Don haka idan har kabilun yahudawa guda goma sha biyu sun fita daga jikin Annabi Yakuba A.s (Israel), to muna iya cewa kabilar Annabi yakuba da yarensa shine kabila ta ainihi, samammun kabilun kuwa sune waɗanda 'ya'yansa sha biyu da jikikinsa suka ɗauka bayan rarrabuwarsu ga wajen zama
Kuma ana iya samun kabilu sama da ɗaya mai amfani da yare ɗaya, amma dai anfi samun kowacce ɗlkabila da irin nata yaren gami da ɗabi'a wanda take samarwa kanta-da-kanta gwargwadon wurin zamanta da aɓin bukatarta da kuma abubuwa makusanta da take dasu.
   Sannan tana iya yiwuwa ma, kafin Hausa ta zama hausa, sai da wasu kabilu suka firfita daga asalin kabilar ta ainihi. Tunda dai zamu gamsu cewa hausa daga wata kabilar ta cire kanta.
   Kowa dai ya rike cewar Maguzawa sune asalin hausawa, har ana kallon kalmar hausa a matsayin bakuwa. Don haka yadda akayi hasashen alaka ta jini tsakanin kabilun maguzawa, Gwandara, Ngizzim da kuma Bole shima abin nazari ne wajen gane asalin uban jinsi wanda hausawa suka fito daga gareshi, tunda masana sun nuna cewar kwayoyin halittu gami da yaruka duk sunyi kaman-ce-ceniya da juna.
   A Littafin tarihin Gwandara da Dr. Silvestri O. Ayihai ya wallafa mai suna 'The History of Gwandara towns and villages' ya nuna cewar sai da kabilar Gwandara ta jima tana zagaye-zagaye daga nan zuwa can, suna Farauta karkashin jagorancin shugabansu mai suna Dan Baba sannan suka riski wani waje mai suna Kupai sannan suka fara zama. Daga nan ne sannu a hankali suka samar da masarautar su gagaruma.
   Mu kuwa anan kasar hausa, an samu labarin baka cewar asalin Gwandara hausawa ne da suke zaune a kano, wai lokacin da Musulunci yazo sukace sam Gwanda (suyi) rawa da (suyi) Sallah, don haka suka bar kano zuwa wani wajen da zama.
    To idan ma wannan labarin na Gwanda-rawa-da sallah bai inganta ba, wancan binciken na kwayoyin halitta ya isa ya nuna mana cewar zamani mai tsawo daya gabata kabilun biyu sun zauna da juna a matsayin yanuwan juna.
   Kabilar Ngezim kuwa ance sune asalin wadanda suka soma zama a tsohon birnin Ngazargamu na daular Kanem. Suma dai ance sun warwatsu a wannan yanki da hausawa suka mamaye ayau, amma dai yankunan Yobe, Borno da Jigawa nan ne tsohon wurin zamansu.
    Haka ma kabilar Bole, wadda  akace suma mafarauta ne waɗanda suka mamaye yankunan Bauchi, Gombe, Yobe da kuma Jos. Zuwa yanzu ana ganin kamar sun saki al'adunsu da yarensu sun ɗauki na hausawa.
  Su kuwa maguzawa ance manoma ne, amma tana iya yiwuwa sun jarraba noma ne sukaga yagi farauta riba don haka suka yadda sana'ar kakannin nasu.
   To ai waɗanda suka fara zama a dutsen dala na garin kano ma ance mafarauta ne.. Wai har taron shiga farauta ma akeyi a bakin dutsen lokaci zuwa lokaci, inda manyan mafarauta ke zuwa daga sassa mabanbanta.. Kenan farauta sana'ar kakannin waɗannan alummomin ne baki ɗaya, don haka suka kasa sakinta, tayadda koda sun zauna a wani wuri na wani lokaci sun jarraba wani abin, da zarar sun tashi daga wurin kanta suke sake komawa..

(c) 2017 Taskar Hikayoyi

No comments:

Post a Comment