Tuesday, October 18, 2022

Karen Bana...


Kakana ke ba ni wannan labari.

Wai a wani gari aka yi wani ja'irin maroƙi, wanda kowa ke shayi saboda shaƙiyancinsa. A duk lokacin da maroƙin nan ya sallama wa mutum, to ƙoƙari yake ya samu 'yan sulalla ko rigar da ya ba shi domin su rabu salin alin. 

Ran nan sai maroƙin nan ya kai raraka gidan wani Alhaji, wai shi Alhaji Sule, yana neman sadakar riga. To kowa a garin ya san hannun Alhaji bai saba da miƙawa ba, sai dai karɓa. Alhaji Sule ya yi 'yan dabarunsu na marowata, ya hana maroƙi riga. Ashe maroƙi ya ji haushi, ya lashi takobin shirya wa Alhaji lalata. Ya samu wasu yara ya ba su 'yan kwabbai, ya tsara musu abin da yake so su yi.

To ɗabi'ar Alhaji ita ce kullum da yamma, sai ya fito ƙofar gida, ya harɗe bisa wundi ya kunna lofe, yana tunanin yadda taro zai koma sisi. Ran nan yana kishingiɗe a kan wundi, kamar yadda ya saba, sai ga yara biyu. Da zuwa gaban Alhaji, sai suka sarƙe da faɗa. Maroƙi da ke maƙe yana kallo, ya yi but ya fito da gudu, ya nufo yara yana musu tsawa, "kai, kai, kai! Wane irin rashin hankali ne kuke faɗa gaban mutane, har kuke neman taka musu shimfiɗa? Ka ga lalatattu! Me ya haɗa ku faɗa?"

Yaro ɗaya ya ce, "sulena ya ɓatar."

Maroƙi ya ce, "yanzu saboda sule kuke wannan faɗa? Sulen banza sulen wofi! Me aka yi aka yi sule! Da ku da sulen jakar ubanku! Allah ya tsine wa sule albarka!"

Da Alhaji ya ji cin fuskar ya yi yawa, sai ya tattara 'yar tabarmarsa, yayin da zai shige gida ya dubi maroƙi ya ce, "riga dai ce an hana ka! Zagin da ka yi mini kuma Allah ya isa!"

Karen bana, maganin zomon bana. Rowa ba ta da amfani!

1 comment:

  1. It is how to get a new Weight Loss. Let me to make this crystal clear, here are the most constructive parts of Dietary Supplements. This is true of most of the stories you hear about using Weight Loss to be less commonplace. You may guess that I'm in over my head. It is going to be a lecture on this.

    https://www.nutraket.com/biocut-keto-acv-gummies/

    https://www.nutraket.com/rejuvenate-cbd-gummies/
    https://www.nutraket.com/verti-gummies-reviews/
    https://www.claimhealthy.com/red-boost-reviews/
    https://www.claimhealthy.com/cannutopia-male-enhancement-gummies/
    https://www.offerplox.com/cbd-products/essential-cbd-gummies/
    https://www.offerplox.com/weight-loss/keto-extreme-fat-burner/

    https://usanewsindependent.com/2023/01/viaketo-gummies-reviews-bhb-apple-gummies-holland-and-barrett-via-keto-gummies-scam/
    https://usanewsindependent.com/2023/01/animale-male-enhancement-animal-cbd-gummies-for-men-reviews-2023/

    ReplyDelete