Thursday, May 18, 2017

NAZARI KAN ASALIN HAUSA

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
    08060869978

Kashi na biyu.

ASALIN JINSIN HAUSAWA

Tana iya yiwuwa, littattafan mu na addini sune suka fara kawo mana tarihin asalin jinsi da rarrabuwarsa. Saboda wannan wani tarihi ne daya faru wanda indai ba baiwa mutum iliminsa akayi ba, zaiyi wuya ya iya wassafa yadda tarihin ya faru.

   Ance Annabi Adamu da Matarsa Hauwa'u sune mutane na farko a duniya. Sune suka rinka haihuwar 'ya'yaye biyu-biyu daki-daki, tare da haɗa aure tsakanin mace ɗaya da namiji ɗaya daga tagwaye mabanbanta, watakila wannan haihuwar tasu itace asalin kabilu, gamin gambizar kuwa shine asalin dangantakar jinsi da kuma rarrabuwar sa.

   Idan ma ba haka ba, ko labarin Annabi Nuhu A.S ya nuna cewar ya haifi 'ya'yaye uku ne. ƊAkace Hamu shine ya haifi bakin mutum na farko a duniya, daga jikinsa kuma zuriyar hindu ta fito. Samu shine na biyu wanda akace daga jikinsa turawa suka fito, sai kuma Yafisu wanda akace daga tsatson sa kabilun birnin Sin suka ɓulɓulo. Don haka, tanan kaɗai muna iya hasashen cewa cakuɗuwa ta silar auratayya da sauran kabilu ne silar haifar da wasu sabbin kabilun.

   Babban labarin dai shine, akwai ilimi na zamani dake bada damar fahimtar kwayoyin halitta tayadda har ake gane wane nada alaka ta jini da wane, da haka kuma muke son fahimtar hausawa da asalin waɗanda suke da alaka dasu, in yaso daga bisani sai mu kwatanta kokarin bin diddigin shekarun da rarrabuwa ta auku a tsakanin su.

   A bisa wancan ilimi na kwayoyin halittu (Genetic), dukkan wani ɗan adam dake doron kasa nada kwayoyin halitta waɗanda ana iya cewa kashi 99.5 na zubin kamanceceniyarsu ɗaya yake da juna. Wannan ke tabbatar mana da wancan ilimin da aka saukar mana cewa mutum ɗaya ne asalin ɗaukacin mutanen duniya, daga gareshi dukkansu duka fito.

   Abu na gaba shine, kusan muna iya cewa a yanzu babu wata kabila da zaka samu 'yan cikinta da kwayoyin halitta zubi ɗaya tsura, sai dai zaka samu kaso sama da hamsin iri kaza ne, sannan da wasu kashe-kashen na sauran kabilu kaɗan-kaɗan aciki.

  Wani masani Ronald Fisher yayi bayani gwargwadon yadda zamu gane bisa tafarkin masanin ilimin kwayoyin halitta Gregor Mendel a littafinsa mai suna 'The Genetical theory of Natural Selection' inda yake cewa dalilai biyu ne kesa wannan cuɗanyar tsakanin kwayoyin halittu. Dalili na farko shine, yanayin yadda ake gadon su kansu kwayoyin halitta na sanyawa na wancan yasha banban dana wancan koda kuwa uwa ɗaya uba ɗaya suke, domin ko a siffance, akan iya ganin uba da 'yayansa uku, yaro na farko yayi kama da mahaifiyarsa, na biyu yayi kama da ubansa, yayinda na uku ya ɗauko kamannin kakansa.  

Dalili na biyu kuwa shine cuɗanyuwar kwayoyin haluttun ta hanyar auratayya. Watau, ɗan wannan kabila ya auri yar waccan kabila. Sai kaga kwayoyin halittar waccan kabila dana wancan sun haɗu a kabila ɗaya, amma sai akalli inda sukafi rinjaya ayi hukunci dashi.

   ASALIN JINSIN LARABAWA DA YARABAWA

   Yana da kyau, kafin mu fahimci asalin jinsun mu mufara fahimtar ilimin dake cikin asalin kabilu makusantan mu.
  Su dai larabawa, wani bincike mai taken 'National Geographic's Genographic' da aka gudanar a shekarar 2005 ya bayya cewa akalla duk wata kabila balarabiya ta fito daga cikin yankuna huɗu ne.

  Yanki na farko shine Arabia.

   Yanki na biyu shine Arewacin Afirka.

   Yanki na uku shine gabashin Afirka.

  Sai yanki na huɗu watau Asia.

  Sai wannan binciken ya ɗauki wasu kasashen larabawa tare da bayyana yadda asalin su ya kasance.

  Misali, Daga ciki an ɗauki kasar Tunisia, wadda akace kaso 88 na kwayoyin halittar mazauna kasar ya nuna cewar suna da alaka ta jini da sauran larabawan Arewacin Afirka. Amma akwai sirki na larabawan Arabia da kaso 5, da sirki na turawa da kaso 4, da kuma sirkin bakaken fata mazauna afirka ta yamma da kaso 3. Wannan sirkin  nuna cewar an samu auratayya da gamin gambizar kwayoyin halittu shekaru da dama da suka wuce a tsakanin jinsosin da aka zayyana a sama.

   Labarin kusan haka yake ga Yarabawa domin kuwa wani bincike da wasu masana Adebuwale Adeyemo na jamiar Ibadan, Chenchen Yianxiu na Cibiyar bincike ta 'National Human Genome' da kuma Charles Rotimi na jamiar Horward suka gudanar, sun samu cewar kwayoyin halittun Yarabawa, ɗaya ne dana kabilun Igbo, Akan, da Gaa-Adangbe.

   Hakan na iya nufin cewar Asalin kabilun mutum ɗaya ne, daga 'ya'yansa ko jikokinsa aka samu rarrabuwar waɗannan kabilu har ma dana yare, tunda binciken yayi hasashen cewa duk yarukan kabilun suna da alaka da juna, asalinsu guda ne, daga bisani suka rarrabu, duk da dai binciken bai nuna sauran kabilun da suka shigar da kwayoyin haluttun su cikin na waɗannan ɗinba.

  JINSIN HAUSAWA


Abinda wani bincike dangane da bakaken fata yayi hasahe shine shekaru masu yawa da suka gabata, mafi yawan bakaken fata suna wuri ɗaya ne a zaune, kuma tana iya gaskatuwa Cewa mutum ɗaya ne uba wanda daga jikinsa duk kabilun bakaken fata suka fito. Amma dai, anyi hasashen cewa tun shekaru dubu sittin zuwa dubu tamanin baya bakaken fata suka soma baro wancan mazaunin nasu na asali tare da fantsamuwa a sassan duniya musamman afirka ta yamma. Daga waɗannan zuriyar ne kuma akafi kyautata zaton bakaken fata Hausawa sun fito.

   Babu jimawa, farfesa Umar Elzakzaky Al-Bahaushe yayi hasashen cewa kwayoyin halittun hausawa dana tsoffin misirawa sunyi kamanceceniya, har ma yace yana kallon kamar firaunan dayayi zamani da Annabi Musa A.S bahaushe ne.

  Inaga zamu karu da ilimi idan muka kalli zancen nasa da kuma martanin hujjoji da masana suka bashi dangane da musanta wannan magana tashi...

Za mu ci gaba.

(c) 2017 Taskar Hikayoyi

No comments:

Post a Comment