Littafi ne da ya kunshi sabuwar fassarar dadadden littafin Larabawan nan mai suna ALFULAYLAH WA LAYLAH. An inganta fassararsa da daidaitacciyar Hausa, da kowane Bahaushe zai iya karantawa kuma ya fahimta.
Littafi ne da ya kunshi hikayoyi masu ratsa zukata, wadanda suka kunshi, tsantsar soyayya, jaruntaka da yaki, tsafe-tsafen mutanen dauri, duniyar aljanu da maridai, tatsuniyoyi, wa'azi da nasihohi, makirce-makircen maza da mata. Littafin ALFULAYLAH tumbin giwa ne, wanda babu irin labarun da babu a ciki.
Tuni mujalladi na farko ya shiga kasuwa. Maza hanzarta domin ku mallaki naku. Za a same shi a manya da kananan kantunan sayar da littattafai.
Haka kuma ga masu son karanta littafin dukkansa a Facebook (tun daga dare na 1 har zuwa dare na 1001), mun zube shi a cikin zauruka (groups) goma sha bakwai a Facebook, wanda za a iya biyan Naira dari biyu kacal (N200) domin shiga kowane zaure. Kada ku bari wannan dama ta wuce ku.
A tuntubi daya daga cikin masu fassarar, domin karin bayani game da yadda za a samu littafin, ko yadda za a biya kudin rijista:
Farfesa Malumfashi:
08035924022
Danladi Z. Haruna:
08030764060
Bukar Mada:
08021218337
To allah ya taimaka
ReplyDeleteThis comment has been removed by the author.
ReplyDeleteNa Dade ina kewan sanin karshen labarun dare dubu da daya sai yanzu Allah ya nufa zan samu.Allah ya saka muku da Alheri ya Kuma kara muku basira da nissan kwana Amin.
ReplyDeleteNa Dade ina kewan sanin karshen labarun dare dubu da daya sai yanzu Allah ya nufa zan samu.Allah ya saka muku da Alheri ya Kuma kara muku basira da nissan kwana Amin.
ReplyDeleteTo wai, muda muke nesa daku sosai, yaya za'ayi mu sami littafin a hannu? Musamman mu da muke nan jahar kebbi!?
ReplyDeleteWadanne shafuka ne zamu samu labarin?
ReplyDeleteKu bamu sunayensu