Sunday, May 14, 2017

TARIHIN GOBIR: DA YADDA GOBIRAWA SUKA RISKI KASAR HAUSA

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

  Kasar gobir na ɗaya daga cikin kasashen hausa na ainihi, ance ita ɗin tsohuwar daula ce kuma wata babbar kasa ce da tayi iyaka da Agades daga arewa, tayi iyaka da Zamfara daga Kudu, tayi iyaka da Mayali daga Gabas, sannan kuma daga yamma  tayi iyaka da Konni.


    Amma magana anan itace, asalinsu ba hausawa bane tunda wasu nacewa asali waiƴ daga gabas ta tsakiya suka fito musamman ma Misira, inda ake da yakinin cewa Sarakuna ukku daga cikin sarakunan Misira gobirawa ne.

Sarkin Gobir Mai daraja Alhaji Abdulhamid Balarabe Salihu ya taɓa faɗar asalinsu a wata fira da jaridar 'Daily Trust' tayi dashi, shine yake cewa:

  Gobirawa sun zone daga misira (egypt). Har Yace su jikokin Annabi Nuhu A.S ne kuma sun bar misira saboda wahalar mulki na sarakunan lokacin. Shine suka sauka a wani wuri mai suna Gubur. Daga nan ne suka samo sunan Gobir.

  Yaci gaba da cewa daga baya sun isa Yemen, sunyi yaki sosai a kasar saboda su suna da jinin yaki da jarumta. Daga nan kuma sai suka isa libya, a haka suna matsawa har suka zo wani gari mai suna Azbin inda yanzu mutanen Taureg suka mamaye.

   Da suka bar Azbin sai suka shiga sahara, har suka kafa wani gari mai suna Magali, daga baya sai suka bar garin izuwa wani mai suna Surukul (dukkansu yanzubsuna jamhuriyar Niger ne). A hankali suka riski birnin lalle da gwararramu a karni na 15 zuwa na 16. A lokacin kuwa, Sarkin zamfara Abarshi ke mulki wanda yake da zama a Katanga, kuma an samu har ya auri ɗiyar sarkin Gobir mai suna Fara, wadda ta haifi Sarkin gobir Ibrahim Babari.

    Kafin Babari ya zamo sarki, ai sai dayayi faɗa da Sarkin Zamfara na lokacin kuma yaci karfinsa. Akan haka sarkin Zamfara ya kuduri niyyar halakashi, amma sai yayarsa ta maido dashi kasar mahaifiyarsu watau Gobir, a haka kuma har ya zama sarki (Watau yayi gado ta wajen Uwa).

   Babari ya roki Sarkin gobir ya bashi wuri a yankin Zamfara inda zai zauna, amma sai aka gargaɗi sarkin Zamfara da cewa kul ya baiwa Babari gurin zama domin nan gaba zai iya mamaye zamfara dukkan ta, ai kuwa daga bisani hakan ne ya faru, da yaki ya ɓarke a wajajen karni na 16 zuwa na 17, sai da Goburawa suka cinye har Alkalawa da yaki. (abinda ke nufin inda suke zaune ayau asali kasar zamfara ce)

   Sarkin Gobir Abdulhamid ya kara da cewa " A lokacin Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo (Karni na 17), ance an ruwaito cewa Ko zakaru basa cara sabida jarfin tsafinsa, kuma aduk yake-yaken da sukeyi, gobirawa basu taɓa mika wuya ba. Ance sunfi gwammacewa a kashe su akan su mika wuya, shiyasa ake musu kirari da 'Gobir gidan faɗa'.

     Sarkin yace " Bawa jan Gwarzo bai taɓa yaki da Shehu Usmanu ba A zamanin jihadi, maganar gaskiya ma itace shehu ya koyar da 'ya'yan Bawa, ciki harda Yunfa, Atiku, Bello da Mayaki. Ance ma saida shehu yayi musu nasiha da kada su bari a samu rarrabuwar kawuna a tsakanin su.

   Sarkin yace " Mutanen dake kusa da Bawa sune suka haɗa kiyayya a tsakanin su, wanda yayi silar shehu yabar Alkalawa, daga baya kuma yaci gaba da jihadi a sassan sokoto.

  Dan gane da tsagun gobirawa, Sarkin yace asali basu da tsagu a fuska, amma sabili da yake-yake ne yasa suka rinka tashi daga nan zuwa can, don haka suka ɓullo da tsagu domin su rinka shaida junansu.

(c) 2017 Taskar Hikayoyi

No comments:

Post a Comment