Saturday, April 29, 2023

ARZIKI RIGAR ƘAYA (1)

HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Sarkin Bagadaza, kuma Sarkin Musulunci, Halifa Haruna Rashid na zaune kan karagar mulki ya harɗe, fadawa kuwa sun kewaye shi ana tsakiyar fadanci sai ga wani saurayin bawa ya shigo riƙe da wata hula da masu mulki ke sanyawa. Ita wannan hula ana kiran ta kambin sarauta. Wannan kambi da bawa ya shigo da shi an ƙera shi da jan zinari aka yi masa ado da lu'ulu'u da jauhari da dukkan duwatsu masu daraja, amma ba a rufe saman shi ba. Wannan kambi babu tamkarsa a wannan zamani, kambi ne da kuɗi ba zai iya saye ba. 

Bawa ya faɗi gaban Sarki ya yi gaisuwa, sa'annan ya ce, "ya Sarkin Musulunci, Uwargida Zubaidatu ce ta aiko ni gare ka da wannan kambi da ta sa aka ƙera mata. Ga shi an kammala ƙera shi, ta nemi jauharin da za a liƙe saman shi, ta kasa samun wanda ya yi daidai a cikin taskarta, duk wanda aka gwada sai a ga ya yi ƙarami."

Sarki ya dubi barori ya ce a tafi a dubo irin jauharin da Zubaidatu ke buƙata. Barori suka zabura da hanzari suka tafi. Can jimawa sai ga su sun dawo. Suka ce wa Sarki, "Allah ya taimake ka, mun duba taskar Sarki duka, amma ba a samu jauharin da ya yi daidai da wannan hula ba."

Halifa ya fusata ya ce, "ta yaya Sarki kamata, wanda ya mallaki sarakunan duniya duka, ɗan ƙanƙanin abu kamar wannan ya gagare ni mallaka. Kaicon ku! Ku tafi cikin kasuwanni, ku binciki dillalai da tajirai da fatake, maza ku nemo wa uwargida abin buƙatarta."

Barori suka fantsama cikin kasuwannin Bagadaza suna cigiya, har Allah ya gajishe su ba su samu jauhari mai girman da suke buƙata ba. Suka dawo gaban Sarki suka ce, "ya Sarkin Musulunci, wannan abu ya wuyata ga tajiran wannan birni da fataken da ke shigowa. Amma an ba mu labari cewa, ba za a samu wannan jauhari gun kowa ba, sai wurin wani attajiri ɗaya da ke zaune a birnin Basara mai suna Abu Muhammad Kasala."

Yayin da Halifa ya ji wannan zance, sai ya umurci wazirinsa, mai suna Ja'afaru al-Barmaki, da ya rubuta takarda zuwa ga Hakimin Basara, Muhammad al-Zubaidi, ya faɗa masa cewa, maza-maza a zo masa da tajiri Abu Muhammad Kasala zuwa Bagadaza.

Nan take Waziri Ja'afaru ya ɗauki takarda da alƙalami ya rubuta saƙon Sarki zuwa ga Hakimin Basara. Ya buga hatimi kan takarda ya naɗe ta, ya danƙa wa Masrur as-Siyafi, babban haunin Sarki. Wanda shi kuma nan take ya yi shiri tare da 'yan rakiya, suka rankaya sai birnin Basara.

Hakimin Basara ya tarye su da murna, ya shirya musu gara, suka sharɓa. Bayan sun huta sai Masrur ya ce wa Hakimin Basara, "to, ba fa zama muka zo yi ba." Ya zaro takarda, ya karanta wa Hakimi saƙon Sarkin Musulmi. Hakimin Basara ya ce, "na ji, na karɓa." Nan take ya shirya wata tawaga ya haɗa su da Masrur suka nufi gidan tajiri Abu Muhammad.

Da isar su gidan sai suka ƙwanƙwasa ƙofa. Wani bawa ya buɗe ƙyaure ya leƙo. Masrur ya ce masa, "je ka wurin ubangidanka ka faɗa masa cewa, Shugaban Muminai na nemansa zuwa Bagadaza."

Bawa ya koma cikin gida. Jim kaɗan sai ga tajiri ya fito. Ko da ya ga Masrur tare da tawagar Hakimin Basara, sai ya faɗi ya yi gaisuwa, sannan ya ce, "na ji, na kuma karɓa kiran Sarkin Musulmi. Amma ba kwa shigo daga ciki ba, ko ɗan ruwa ku kurɓa kafin na kimtsa mu tafi?"

Masrur ya ce, "ai ba dama, sata lahira! Halifa na can na jiran mu. Don haka babu buƙatar ɓata lokaci. Maza shirya ka fito mu tafi, kafin ran Halifa ya ɓaci."

Tajiri ya ce, "to bari na shiya yanzu mu tafi, amma ku shigo daga ciki ku zauna, kun san an ce shirin zaune ya fi na tsaye. Idan na shirya kuma na samu ɗan guzurin da zan kai wa Halifa, domin zuwa da wuri ya fi zuwa da wuri-wuri." Ya yi ta lallashin su dai, har suka yarda suka shiga cikin gidan.

Da kutsa kansu cikin turakar farko ta gidan, sai suka ga an daje duka bangayen nan da labulayyen alharini wanda aka yi wa cin baki da ɗanyen jan zinari, aka ƙawata su da duwatsu masu ƙyalƙali da daukar ido. Abu Muhammad ya umurci ɗaya daga cikin bayinsa da ya kai Masrur bayi, ya yi wanka, ya fitar da ƙurar tafiya daga jikinsa.

Bawa ya yi wa Masrur jagora har zuwa ɗakin wanka. Masrur ya ga ɗakin wankan da bai taɓa ganin irinsa ba. Bangayen ɗakin da daɓensa duka na duwatsu ne masu darajar gaske, waɗanda aka cakuɗa da zinariya da azurfa. Ruwan wankan kuma an gauraya su da ruwan wardi.

Bayi suka himmatu wajen yi wa Masrur da 'yan rakiyarsa hidima yayin da suke wanka. Da suka gama wanka, aka ba su tufafi na alfarma, waɗanda aka yi wa ado da kumfar zinari yayin saƙa su, suka sanya.

Bayan Masrur da 'yan rakiyarsa sun kimtsa sai suka nufi inda Abu Muhammad Kasala ke jiransu, suka tarar da shi zaune bisa wani dandamali da aka yi cikin turakarsa. A saman wannan dandamali aka girke wata ƙatuwar kujera mai kama da gado, wadda aka shinfiɗa wa katifu, aka lulluɓe katifun da zannuwan alharini. A saman wannan kujera maigidan yake zaune. Bangon da aka jingina kujerar kuma an lulluɓe shi da labulen hatsaya da alharini da aka saƙa su tare da zinariya, aka kuma lilliƙa masa duwatsun jauharai masu launi daban-daban.

Sa'adda Masrur ya shigo cikin turakar, sai Abu Muhammad ya sauko daga kan kujera, ya tarye shi da fara'a, ya sake yi masa maraba. Ya ja shi suka koma kan kujearar suka zauna wuri guda, sauran mutane kuma suka zauna kan kujerin da ke cikin turakar. Daga nan mai gida ya yi umurni da a fito da abinci da abin sha. Nan da nan bayi da kuyangi suka yi ta jido akussan abinci da gorunan abin sha suna girkewa a gaban baƙin nan.

Masrur ya saki baki yana tu'ajjibin kyawun akussan da aka kawo musu abinci a ciki, su dai ba daga itace aka sassaƙa su ba, ba kuma da dutse aka yi su ba, to ko da ƙashi aka yi su? Oho. Ya ce a ransa, 'na rantse da Allah ban taɓa ganin akussa masu kyau kamar waɗannan ba, waɗanda babu irinsu ko da a fadar Halifa.'

Kowane akushi da irin abincin da ke cikinsa, wani an zuba soyayyen nama, a wani kuma an zuba dafaffe. A wani akushin kuma an zuba farar shinkafa da zuma, wani kuma gurasa ce da miya. Aka dai girke musu abinci iri daban-daban. Suka fara ci suna taɗi, suna annushuwa, ba su farga ba har dare ya ƙwace musu. Da za su koma masauki, Abu Muhammad ya ba kowannensu dinari dubu biyar.

Washegari kuma ya ƙara yi musu kamar yadda ya yi musu jiya. Ya tufatar da su tufafi na alfarma, masu launin kore da ruwan zinari. Ya himmatu ga yi musu hidima. Da Masrur ya ga suna shirin shantakewa, sai ya ce wa Abu Muhammad, "ya kamata ka shirya mu tafi, kada Halifa ya ga mun daɗe, ransa ya ɓaci."

Abu Muhammad Kasala ya amsa masa da cewa, "ya shugabana, yi haƙuri dai ka jinkirta mini, zuwa gobe na gama duk shirin da nake yi, sai mu tafi." Don haka suka sake kwana ɗaya. 

Da gari ya waye, Abu Muhammad ya sa bayi suka shirya masa wata alfadararsa da yake hawa. Sirdin da aka ɗaura wa alfadarar da sauran kayan da aka shirya ta da su duka an yi su ne daga zinariya da azurfa da lu'ulu'u, sai ɗaukar ido suke yi cikin rana. Masrur ya dubi alfadarar nan, ya ce cikin ransa, 'zan yi mamaki idan har Halifa bai tuhumi Abu Muhammad yadda ya yi wannan arziki, idan ya je masa da tarin dukiya haka.' Daga nan suka yi sallama da al-Zubaidi, suka fita daga Basara suka fuskanci Bagadaza. A kwana a tashi, ba tare da sun tsaya ko'ina ba, har Allah ya kai su birnin Bagadaza, gidan aminci.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, in sha Allah.

Bukar Mada
29/04/2023